Kashe Malami a Zamfara: An Shiga Rudani
Al'ummar garin Mada da ke Gusau a jihar Zamfara sun shiga wani hali bayan sun wayi gari da labarin mutuwar limamin masallacin garin, Abubakar Hassan Mada.
Wasu mazauna garin sun shaida wa BBC cewa an tsinci gawar limanin ne, bayan wasu sanye da kayan sabuwar rundunar tsaron jihar sun tafi da shi a ranar Talata.
Sai dai bayan wani lokaci an tsinci gawar malamin bayan an yi masa yankan rago.
Ɗaya daga cikin mutanen garin na Mada ya shaida wa BBC cewa "Jiya da yamma bayan sallar la'asar wasu sane sa kaya irin na asakarawa suka shigo, an ce mana daga yankin Tsafe suke, sai suka haɗu da askarawa na nan Mada, suka nuna musu gidan liman Abubakar Hassan Mada,"
Ya ƙara da cewa "Bayan da suka fita da shi wajen gari sai suka tsaya suka yi masa yankan rago."
Mutum na biyu da BBC ta zanta da shi wanda shi ma mazaunin garin na Mada ne ya ce: "sun zo sun tafi da shi har suna dariya suna raha, ba mu yi tunanin wani abu ne maras kyau zai faru da shi ba".
Mun fara bincike - Kwamandan Askarawa
Sai dai a nasu ɓangaren, rundunar Askarawar Zamfara sun bayyana wa BBC cewa suna bincike kan kisan malamin.
A tattaunawar sa da BBC, kwamandan Askarawan Zamfara, Kanar Rabiu Ƴandoto mai murabus ya ce ya zuwa safiyar ranar Laraba hukumar ta fara bincike a kan lamrin.
A cewarsa: "Mun sa a tattara dukkanin Askarawan yankin Mada domin yin bincike game da kisan limamin."
Sai dai ya bayyana wa BBC cewa doka ba ta bai wa wani ba'askare damar ɗaukar doka a hannunsa ba, koda kuwa ya kama wanda ake zargi da laifi.
Mada na cikin yankunan jihar Zamfara da suke fama da mummunar matsalar ƴan fashin daji masu kashewa tare da garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.
managarciya