Tsohon shugaban Ƙaramar hukuma ya bar PDP zuwa APC a Sakkwato

Tsohon shugaban Ƙaramar hukuma ya bar PDP zuwa APC a Sakkwato
Tsohon shugaban karamar hukumar Isa  Alhaji Alhaji Abubakar Yusuf Dan'ali ya bar jam'iyar PDP ya koma APC a jihar Sakkwato.
Mataimaki ga Sanata Ibrahim Lamiɗo a kafafen yada labarai Auwal Nasir ne ya sanar da hakan ya ce Sanata Lamiɗo ya karbi tsohon shugaban karamar hukuma wanda yake jigo ne a jam'iyar PDP in da ya dawo APC a ranar jumu'a.
Sanata Ibrahim dan majalisa ne da ke wakiltar Sakkwato ta Gabas a majalisar dattijai ya nuna farin cikinsa ga cigaban da jami'iyarsa ta samu.
Abubakar Yusuf ya ce ya koma APC ne a tafiyar Sanata Ibrahim Lamiɗo don gamsuwa da yanda yake tafiyar da wakilcinsa ga mutanensa.
Ya ce Sanata ya kawo cigaba a tafiyar matasa da bunkasa karatunsa da kula da tsaro a yankinsa.
Shugaban matasan tafiyar tsohon shugaban ƙaramar hukumar Haliru Bara'u Dankawu ya ce yanzu ne yake jin maganar komawar mai gidan nasu zuwa APC  a wurin wakilinmu, kan haka bai yi matsaya ba.