Jam'iyar PDP a jihar Sakkwato ta karbi 'yan kasuwa 1,868 dake cikin kungiyoyin 'yan kasuwa 10 da suka bar jam'iyar adawa ta APC suka koma PDP a jihar.
Sun ce sun sauya shekar ne domin kyakkyawan shugabanci na Gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal.
Shugabna kungiyar masu yin kujeru da gadaje na jiha Alhaji Lawali Aminu Lalala amadadin wadan da suka sauya shekar ya ce sun gamsu da yadda Tambuwal ke jagoarncin Sakkwato a karkashin PDP hakan ya sa suka shigo tafiyar domin a ciyar da jihar Sakkwato gaba.
Ya ce gwamnatin APC da suka zaba a Nijeriya ta kasa a dukkan bangarori, don haka muka goyi bayan PDP kuma za mu zabi 'yan takararta a zabe mai zuwa.
A bayanin da sakataren yada labarai na jam'iyar PDP Hassan Sahabi Sanyinnawal ya fitar ya ce a lokacin karbar masu sauya shekar Shugaban jam'iyar PDP Bello Aliyu Goronyo ta bakin mataimakin shugaba na yanki Muhammad Dangwaggo ya tabbatar musu su cikkakkun 'yan jam'iya ne ba su da bambanci da wadanda suka tarar.
Dan takarar gwamna a jam'iyar PDP Malam Sa'idu Umar Ubandoma ya yi masu alkawalin tafiya tare da su a lokaci da bayan kamfe.
Ya yi kira da su yi aiki tukuru don tabbatar da nasarar PDP a dukkan matakai.