FRIED SUPERGETTI, Sirrin Taliya Da Yakamata A Sani

Girki mai matuƙar ɗanɗano da gamsarwa. Supergetti abinci ne mai inganci a lafiyar mutane musamman in aka yi la'akari da kayan haɗinsa. Taliyar tana ƙosar da mai cinta a cikin sauƙi ba tare da ya wahalar da gaɓoɓinsa ba. Taliya abinci ne da ya dace da kowane gida a saboda zamansa matsakaicin abinci ba 'ya macen da ba ta iya girka shi ba. Taliya ce mafi sauƙin ci a dukkan nau'o'in abincin Hausa Fulani duk da tana cikin abincin da ya zo masa daga waje amma yanzu ya koma nasa. Masana kiyon lafiya ba su sanya Taliya cikin abinci mai haɗari ba, hasalima ba wani mai nau'in ciyo da aka hana shi cin Taliya.

FRIED SUPERGETTI, Sirrin Taliya Da Yakamata A Sani

KAYAN HADI:

*Supergetti
*Nama (kaza ko zabo)
*Jajjagaggen tattasai da tarugu
*Maggi
*Curry
*Bakin yaji(Black papper)
*Man gyaɗa
*Albasa
*Lawashi
*Tafarnuwa

YADDA ZAKI HAƊA:

Da farko za ki samo supergettinki ki kakkarya ta dai dai yanda kike so.
Sai ki ɗora ruwa a tukunya ki zuba supergettin a ciki da ɗan mai kaɗan (amfanin man don ya hana taliyar damƙewa).
Idan ta dahu sai ki ɗauke ki juye a kwando ta tsane, sai ki barta ajiye ki koma kan kayan miyanki.
Za ki zuba jajjagaggen kayan miyanki a wata tukunyar sai ki ɗora a wuta, ki barsu su tsane ruwan jikinsu sai ki zuba man gyaɗa ki fara soya kayan miyan sama-sama.
Sai ki zuba Maggi, curry, baƙin yaji da sauran kayan ƙamshin da kike ra'ayi sai ki ci gaba da soyawa.  Sai ki zuba yankakkiyar albasarki da kika yiwa yankan rings da lawashi a kai. Ki ci gaba da soyawa.
Idan kina da ruwan nama za ki iya zuba kaɗan sai ki kawo soyayyen naman kazarki kona zabo ki zuba a cikin kayan miyan ki ci gaba da soyawa.
Idan ta soyu sai ki ɗauko supergettinki ki dinga zubawa ciki a hankali kina juyawa har ki juye duka. Ki ci gaba da juyawa ki tabbatar taliyar ta haɗe jikinta sosai gudun kada ta fito kala biyu. Idan ta soyu sai ki sauke ki juye a mazubi mai kyau ki ɗauko sauran namanki ki jera a kai.

ENJOY

Sirrin Taliya da yakamata a sani

Supergetti abinci ne mai inganci a lafiyar mutane musamman in aka yi la'akari da kayan haɗinsa.

Taliyar tana ƙosar da mai cinta a cikin sauƙi ba tare da ya wahalar da gaɓoɓinsa ba.

Taliya abinci ne da ya dace da kowane gida a saboda zamansa matsakaicin abinci ba 'ya macen da ba ta iya girka shi ba.

Taliya ce mafi sauƙin ci a dukkan nau'o'in abincin Hausa Fulani duk da tana cikin abincin da ya zo masa daga waje amma yanzu ya koma nasa.

Masana kiyon lafiya ba su sanya Taliya cikin abinci mai haɗari ba, hasalima ba wani mai nau'in ciyo da aka hana shi cin Taliya.

Taliya ce abincin da gwanewar mace a girki ke sa a ci ba tare da ƙyama ba.

Tana cikin abincin da ke tona asirin ƙwarewar  mace a fannin girki.


RUKY'S BAKERY