Bafarawa Ya Caccaki  Buhari Kan Kone Mutane A Sakkwato Amma Ya Tafi Legas Bikin Kaddamar Da Littafi

Bafarawa Ya Caccaki  Buhari Kan Kone Mutane A Sakkwato Amma Ya Tafi Legas Bikin Kaddamar Da Littafi

Tsohon gwamnan Sakkwato Attahiru Dalhatu Bafarawa ya bayyana ɓacin ransa a kan Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari sakamakon  rashin zuwa ya jajantawa al'ummar jihar kan ƙona matafiya 25 da 'yan ta'adda suka yi don bai dauki rayuwar mutanen da daraja ba.

 

A wata hira da BBC Hausa ta yi da shi a jiya Asabar, Bafarawa ya ce Buhari ya gaza magance rashin tsaro da ke addabar jihohin Zamfara, Sokoto da Katsina.

 
Bafarawa ya baiyana cewa shugaba Buhari ba ya daraja rayukan al'ummar da su ka zaɓe shi, a lokacin neman kuri'a yakan zo wurinsu yanzu da ya samu nasara ya fita batunsu.
 
"Abin da ya fi damu na shi ne yadda a ka maida rayukan al'umma basu da wata daraja. Ka duba rayukan da su ka salwanta a kwanaki 5 ko 6 da su ka gabata.
 
"An harbe mutane sannan an ƙone su a cikin mota amma Buhari ya tafi  Legas bikin ƙaddamar da littafi, littafin da ba Kur'ani ko Bible ba.
 
"Bai zo Sokoto ya yi mana ta'aziya ba sai dai kawai ya turo wakilai.Lokacin da ya ke kamfen neman zaɓe ai da kansa ya zo, ba aikowa ya yi ba, sabo da ya na neman kuri'a.
 
"Me ya hana shi zuwa yai mana ta'aziya da jaje, amma ya tafi Legas wajen kaddamar da littafi? Mu dai kawai sai dai mu ce  Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’un, a Sabon Birni, Shinkafi, Goronyo na cikin mawuyacin hali.
 
"Mu dai kawai sai dai mu ci gaba da addu'a a kan Allah Ya yaye mana Ya kuma kare mu," in ji Bafarawa.
Tsohon Gwamnan ya nuna bacin ransa matuka kan halin da tsaron jihar ya samu kansa mahunkunta sun yi shiru.