FRIED BEANS

     FRIED BEANS
BASAKKWACE'Z KITCHEN
 
    
 
 
 
 
     FRIED BEANS
 
 
INGREDIENTS
Wake
kanwa
tattasai
koren wake
kabewa
albasa me lawashi
maggi
kayan kamshi
mangyaɗa.
 
 
METHOD
Da fari aunty na za ki gyara waken ki,ki cire duk wani dauɗa,ki zuba a ruwa ki wanke,ki sa a wuta ki zuba kanwa ko baking powder  ya dahu,ba luguf ba,tunda ba fate yi zaki ba,bayan ya dahu bai farfashe ba,se ki tsane shi a matsami,ki kara wanke shi,ki barshi ya ɗige a cikin kwando.
Sai  ki ɗauko tukunyar ki ,ki zuba kayan miya,maggi gishiri da man gyaɗa,ki soya kayan miyar ya kone kamas,se ɗauko waken ki da ya tsane,se ki zuba ki jujjuya ya gauraye ko ina,kar ki cika kayan miya fa,gudun kar ya caɓe ya zama fate,se ki ɗauki yankakken tattasan ki da albasa ne lawashi da kika yanka,da kabewar ki da ki ka riga kika dafa ta sama sama se ki zuba ki juya ki sauke ,sai ci kawai.
 
 
MRS BASAKKWACE