Kwamishinan 'yan sandan Zamfara  ya gargadi masu tayar da kayar bai a jihar

Kwamishinan 'yan sandan Zamfara  ya gargadi masu tayar da kayar bai a jihar
Kwamishinan 'yan sandan Zamfara  ya gargadi masu tayar da kayar bai a jihar

 
Anyi kira ga  maharan  daji  da ke addabar jihar Zamfara  da su rungumi shirin gwamnatin jihar na sulhu, kuma su  mika makamansu ko kuma su dandana kudar su nan ba da jimawa ba.
 
 Sabon kwamishinan 'yan sandan jihar Zamfara CP Ayuba Elkana  ya yi wannan gargadin a wani taron manema labarai da ya kira a Gusau, in da ya bukaci 'yan bindigar da su rungumi shirin zaman lafiya da gwamnatin jihar ta fara.
 
 “Dabararun da 'yan sanda za su bi domin kakkabar yan ta'addan shi ne na tattara  bayanan sirri, leken assiri da dai hanyoyin da ya kamata mubi don magance rashin tsaro a fadin jihar.
 

 "Za mu kasance masu mayar da himma don karfafa  dabarun yaƙi da aikata manyan laifuka da tabbatar da samun hadin kan  jama'a, a cikin sha'anin tsaro.
 
 “Jajircewa da za mu yi a  matsayin mu na jami’an‘ yan sanda zai  kasance kan karfafa ingantaccen tsarin tsaro  wanda Sufeto Janar na ‘yan sanda ya tsara da kuma ci gaba da zaman lafiya da Gwamna Bello Matawalle ya fara.
 
 Elkana ya ce "Wannan shi ne babban burina a duk lokacin da nake kwamishinan 'yan sanda a jihar."
 
Kwamishinan 'yan sandan ya yi kira ga sauran jama'a da su taimaka wa 'yan sanda da sauran hukumomin tsaro da ingantattun bayanai kan ayyukan masu aikata laifuka a jihar.
 
 “Yan sandan da ke kula da sassa daban daban za su cika aikin da aka ba su tare da tanadin tsarin mulki da sauran kyawawan dabi’un rundunar.
 
 "Ba za a lamunta da duk take hakkin dan adam ba, cin hanci da rashawa da sauran ayyukan da ba su da nasaba da aikin mu ba,"  in ji shi
 
 Elkana ya yabawa 'yan jarida a jihar kan yadda suke ci gaba da marawa rundunar baya wajen inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

 
 "'Yan jarida mutane ne masu ban mamaki.  Ba za a iya ƙara jaddada gudummawar da ku ke bayarwa wajen gudanar da ayyukan ku ba.
 
 “Don haka ina mika godiya ta ga dukkan ku kuma ina rokon ku da ku kara himma ta hanyar ci gaba da kasancewa tare da hadin gwiwar‘ yan sanda da sauran jami'an tsaro.