Shugaban Majalisar Dattawa Ya Taya Shugaban Kasa Buhari Murnar Cika Shekaru 79 Da Haihuwa 

Shugaban Majalisar Dattawa Ya Taya Shugaban Kasa Buhari Murnar Cika Shekaru 79 Da Haihuwa 

Daga Babangida Bisallah, Abuja

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya aike da sakon taya murna ga shugaban kasa Muhammadu Buhari a bisa zagayowar ranar haihuwar sa. 

Lawan ya yaba da kyakykyawan shugabancin na shugaba Buhari da hangen nesan sa wajen kokarin sa na inganta rayuwar yan Najeriya. 

Ola Awoniyi Mai ba shugaban majalisar dattawa shawara akan aikin jarida Ola Awoniyi ya bayyana sanarwar a wata takardar manema labarai da ya fitar jiya alhamis.
Yace, "ina bin sahun dimbin yan'uwana yan Najeriya da sauran  masu fatan alheri daga ko ina a duniya wajen yi ma Allah godiya bisa ga baka koshin lafiya da tsawon rai. 
"Wannan kyauta ta ubangiji ta ba maigirma shugaban kasa damar cigaba da samar da ingantaccen shugabanci ga kasar mu a wannan lokaci  da duniya ke fuskantar kalubale dabam dabam. 
"Ka kasance shugaba wanda ke da karfin halin gudanar da hangen nesa da jajircewa wajen aiwatar da manufofi don amfanar al'umma. 
"Mai girma, kamar yadda wadanda suka yi aiki da kai suka sani, nima shaida ne akan ka wajen ganin kasar nan ta samu hadin kai, tsaro da cigaban Najeriya. 
"Wannan halayar, hadi da inganta ayyukan more rayuwa, zamantakwa da canza fasalin tattalin arziki zai inganta kwararan ayyukan da zaka bari a matsayin ka na shugaban Najeriya na dabam. 
"Jam'iyyar mu ta APC ta yi sa'ar samun ka a matsayin shugaban mu a wannan gaba ta tarihin ta. Shugabancin ka mai cike da hangen nesa ya samar da hadin kai da dunkulewar jam'iyar, ya kuma taimaka matukagaya wajen sa APC ta zama jam'iyar da jama'a suka fi so don kashin kansu. 
"Shugaban kasa, Allah ya albarkaci Najeriya da shugabancin ka domin ya ba yan kasa da ma'aikatun gwamnati karfin gwiwar fuskantar kalubalen da muke fuskanta da kuma kafa harsashin samar da kasa mai albarka. 
"Majalisar dokoki ta kasa zata cigaba da aiki da kai daidai da tsarin mu da yazo daya da naka don cigaban kasar nan. 
Shugaban majalisar yayi adduar Allah ya kara yi ma shugaban kasa jagora da bashi kariya akan shugabancin shi.