Kotu Ta Yankewa Ɗan Wasa Benzema Hukuncin Ɗaurin  Shekara Guda

Rikicin na Benzema da Valbuena shi ne mafi muni da tawagar kwallon kafar Faransa ta taba gani wanda ya kai ga dakatar da ƴan wasan biyu daga dokawa ƙasar ƙwallo gabanin dawo da Benzema a bana. Masu gabatar da ƙara a zaman kotun na yau a Versailles, sun ce Benzema ya yi amfani da kusancinsa ga Valbuena wajen matsa masa lamba don ganin ya biya masu yi masa barazana da bidiyon batsan kuɗin fansa duk da cewa yana da hannu wajen naɗar bidiyon. Alƙalin ya samu Benzema da laifin hada baki da maras gaskiyan wajen bata sunan Valbuena lamarin da ya sabawa dokokin kasar baya ga kasancewa zambo cikin aminci.

Kotu Ta Yankewa Ɗan Wasa Benzema Hukuncin Ɗaurin  Shekara Guda

Kotu a Faransa ta yankewa ɗan wasan ga bana ƙasar Karim Benzema hukuncin ɗaurin talala na shekara guda bayan samunsa da laifi a yunƙurin ɓata sunan Mathieu Valbuena ta hanyar amfani da wani faifan bidiyon batsa.

A zaman kotun na yau Laraba, wanda Benzema bai halarta ba, kotun ta kuma buƙaci ɗan wasan mai shekaru 33 da ke taka leda a Real Madrid ya biya tarar yuro dubu 75.

RFI ta rawaito cewa Benzema na cikin mutane 5 da aka dawo da shari’arsu cikin watan jiya kan zargin yunƙurin ɓata sunan Mathieu Valbuena tun a shekarar 2015.

Rikicin na Benzema da Valbuena shi ne mafi muni da tawagar kwallon kafar Faransa ta taba gani wanda ya kai ga dakatar da ƴan wasan biyu daga dokawa ƙasar ƙwallo gabanin dawo da Benzema a bana.

Masu gabatar da ƙara a zaman kotun na yau a Versailles, sun ce Benzema ya yi amfani da kusancinsa ga Valbuena wajen matsa masa lamba don ganin ya biya masu yi masa barazana da bidiyon batsan kuɗin fansa duk da cewa yana da hannu wajen naɗar bidiyon.

Alƙalin ya samu Benzema da laifin hada baki da maras gaskiyan wajen bata sunan Valbuena lamarin da ya sabawa dokokin kasar baya ga kasancewa zambo cikin aminci.

A lokuta da dama dai Benzema na musanta zargin tare da bayyana kansa a matsayin mai ƙoƙarin kare mutuncin Valbuena wajen tilasta shi ya biya kuɗin don kar a bata masa suna.

Tun bayan fara shari’ar dai daga Benzema da ke taka leda da Real Madrid har Mathieu Valbuena da ke taka leda da Olympiakos ta Girka babu wanda ya taba halartar zaman kotun.