Kungiyar Ƙwadago Ta Ƙasa Ta Buƙaci Shugaba Buhari Da Yaƙara Albashin Ma'aikata Da Kashi 50

Kungiyar Ƙwadago Ta Ƙasa Ta Buƙaci Shugaba Buhari Da Yaƙara Albashin Ma'aikata Da Kashi 50

Daga Jabir Ridwan.

Kungiyar kwadago ta Kasa NLC ta bukaci shugaban kasa Muhammadu buhari da yakara Albashin Ma'aikata da Kashi 50.

Wannan dai na kushe ne a cikin wata wasika Mai dauke da kwanan watan 8 ga Watan Augastan shekara ta 2022 da suka aikewa shugaba Buhari a matsayin martani da suka mayarwa gwamnonin jahohi.

A Baya dai an ruwaito cewa gwamnonin kasar nan sunyi tada jijiyoyin wuya kan dole sai gwamnatin tarayya ta cire tallafin man fetur da rage wa'adin ajiye aikin malamai na tsawon shekaru 50 kazalika da rage yawan kashe kudade da Yan majalisar kasa keyi.

Kungiyar hakama ta tuhumi gwamnonin da cewa wannan ba hurumin su bane inda kungiyar ta ayyana cewa duk wani dake goyon bayan wannan yunkurin to ba shakka Baya kishin kasa.

A maimakon rage wa'adin ajiye aikin, kungiyar ta bukaci da a duba a gyara albashin Ma'aikata da Kuma Jin dadin su tareda sama musu ababen more rayuwa domin gudanar da aikinsu yadda Yakamata.

Jaridar Intelregion ta ruwaito cewa kungiyar ta Nuna damuwa matuka kan halinda Ma'aikata suke cikin inda ta alakanta Hakan da tabarbarewa sha'anin aikin gwamnati.