Biyu Babu:Hukumar Zabe Ta Yi Magana Ta Karshe Kan Takarar Lawan Da Akpabio

Biyu Babu:Hukumar Zabe Ta Yi Magana Ta Karshe Kan Takarar Lawan Da Akpabio

 

Hukumar zabe na kasa watau INEC ta ki karbar Ahmad Ibrahim Lawan da Godswill Akpabio a matsayin ‘yan takarar kujerar Sanata a 2023.

PM News ta rahoto Kwamishinan INEC, Festus Okoye yana cewa hukumar zabe ba ta san da zaman Ahmad Ibrahim Lawan da Godswill Akpabio ba. 

Dr. Ahmad Lawan da Godswill Akpabio su na neman kujerar majalisar dattawa na mazabun Arewacin Yobe da Arewa maso yammacin Akwa Ibom.

Rahoton yace takarar manyan ‘yan siyasan sun gamu da cikas bayan da hukumar zabe mai zaman kanta tace jam’iyyar APC ba ta da ‘yan takara. 

Tun 2007, Lawan yake Sanatan Yobe ta Arewa, a 2019 ya zama shugaban majalisa. Akpabio ya rike kujerar Sanatan Akwa Ibom daga 2015 zuwa 2019.

Okoye yace APC sun gabatar da sunayen wadannan mutane a matsayin ‘yan takaran, amma sun fahimci ba su ne suka lashe zaben tsaida gwani ba.