Home Labarai Tinubu ya amince da kafa sabuwar bataliyar sojoji a Kwara

Tinubu ya amince da kafa sabuwar bataliyar sojoji a Kwara

27
0

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya amince da kafa sabuwar bataliyar sojoji a jihar Kwara domin karfafa tsaro da yaki da ‘yanbindiga, masu garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka.

A wata sanarwa da mataimakin babban sakataren yada labaran Gwamnan Kwara, Mashood Agboola, ya fitar, gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya ce za a kafa bataliyar ne a garin Omu Aran, hedikwatar karamar hukumar Irepodun.

Gwamnan ya yabawa Tinubu bisa amincewa da bukatar, yana mai cewa sabon sansanin sojojin zai kara karfin ayyukan yaki da ta’addanci da masu garkuwa da mutane a jihar.

Ya kuma gode wa babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, da Ofishin Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro da sauran hukumomin tsaro bisa hadin gwiwar da suke yi wajen magance matsalolin tsaro.

Matakin ya zo ne yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro a wasu sassan jihar, musamman a al’ummar Babanla da ke karamar hukumar Ifelodun, inda mazauna ke zargin ‘yan bindiga da ci gaba da kai hare-hare, lamarin da ya haddasa kashe mutum guda tare da yin garkuwa da wani a wani sabon hari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here