Home Labarai An samu maganin ƙarfin Maza ga wani mutum da ya rasu ...

An samu maganin ƙarfin Maza ga wani mutum da ya rasu a Otal a Jigawa

6
0

An samu maganin karfin maza yayin da aka tsinci gawar wani mutum a otel da ke jihar Jigawa

Rundunar ƴansandan Jihar Jigawa ta tabbatar da fara bincike kan mutuwar wani mutum mai shekara 60 da ya rasu a wani otel da ke birnin Dutse, babban birnin jihar, bayan da ya kamu da matsalar numfashi.

Kakakin rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:50 na ranar Talata, lokacin da mamacin ya shiga otel ɗin tare da wata budurwa mai shekaru 20.

A cewarsa, bayan mutumin ya ba da umarnin a kawo masa abinci, sai ya fara fama da matsananciyar wahalar numfashi, lamarin da ya sa aka kira jami’an ‘yansanda.

Ya ce jami’an daga sashen Yalwawa sun isa wurin cikin gaggawa, inda suka garzaya da mutumin zuwa babban asibitin Dutse. Sai dai likitoci sun tabbatar da rasuwarsa bayan an kai shi asibitin.

SP Lawan ya bayyana cewa jami’an ‘yansanda sun killace wurin da lamarin ya faru tare da fara bincike na farko. Ya ce an samu kayan abinci, abubuwan sha, wani magani da ake zargin na ƙara ƙarfin jima’i ne, da kuma wasu kayayyakin mamacin domin a gudanar da binciken kimiyya (forensic) don gano musabbabin mutuwar.

Ya ƙara da cewa an bi duk matakan da suka dace wajen adana kayayyakin da aka samo domin tabbatar da cikakken bincike.

Rundunar ta ce an mika gawar mamacin ga iyalansa domin yi masa jana’iza bayan likitoci sun tabbatar da mutuwarsa tare da kammala matakan da doka ta tanada.

Haka kuma, budurwar mai shekara 20 da take tare da mamacin a lokacin da lamarin ya faru na ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai ta hanyar bayar da bayanan da za su taimaka wajen gano gaskiyar abin da ya faru.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here