Home Labarai Munafukan Sokoto sun yi nadama bayan da Hisbah ta kama su

Munafukan Sokoto sun yi nadama bayan da Hisbah ta kama su

7
0

Hukumar Hisbah ta Jihar Sokoto ta saki wasu matasa da ake zargi da kafa ƙungiyar Munafukan Sokoto bayan sun nuna nadama tare da ba al’ummar jihar haƙuri.

Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Hukumar Hisbah ta Jihar Sokoto ta fitar.

Matakin ya biyo bayan zaman da Hisbah ta yi da matasan tare da iyayensu, hakiman unguwanninsu da malaman unguwanninsu.

Sanarwar ta ce Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Sokoto, Malam Usman Abdullahi Jatau, ne ya jagoranci zaman da aka gudanar a shalkwatar hukumar.

Hisbah ta ce matasan sun bayyana nadamarsu kan abin da ya faru tare da yin alƙawarin daina ayyukan da suka haddasa matsalar.

Hukumar ta ƙara da cewa matasan sun ba al’ummar Jihar Sokoto haƙuri kafin a sallame su bayan kammala zaman.

A kwanakin baya ne dai matasan suka fitar da wani bidiyo inda suke bayyana cewa sun kafa ƙungiyar munafukai ta jihar Sokoto.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here