Gwamnatin Tinubu za ta sake dawo da batun ƙaddamar sabbin dokokin haraji wanda ake zargin zai ƙara tsadar rayuwa ga Talakawan ƙasa.
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta fara nazarin sabbin dokokin haraji na tsawon makonni shida, domin gano giɓin da ke cikin aiwatar da su, magance matsalolin da suka bayyana tun bayan fara amfani da dokokin, tare da duba korafe-korafe da shawarwarin da ƙungiyoyin kamfanoni masu zaman kansu (Organised Private Sector) da sauran masu ruwa da tsaki suka gabatar.
A cewar Gwamnatin Tarayya, bitar za ta mayar da hankali ne kan inganta yadda ake aiwatar da sabbin dokokin haraji, rage matsalolin da suka taso, da kuma tabbatar da cewa tsarin harajin ya kasance mai adalci kuma ya dace da yanayin tattalin arzikin Najeriya.
Sabbin dokokin harajin dai na daga cikin manyan sauye-sauyen da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar domin faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga na gwamnati da kuma inganta tsarin tattara haraji a faɗin ƙasar.
Sai dai kungiyoyin da dama sunyi zargin cewa tsarin dokar haraji zai iya kara tsadar rayuwa ga talakawan ƙasa idan ba ayi taka tsantsan ba.
