Ƙungiyar Ɗalibai Musulmi ta ƙasa MSSN reshen Jihar Neja ta nemi a biya iyalan mutane 37 da suka rasu a hannun Hukumar Tsaro ta Civil Defence a birnin Minna diyya.
Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Shugaban MSSN reshen Jihar Neja, Mahmud Lawal Murshid, ya fitar a ranar Juma’a, 18 ga Satumba, 2026.
Sanarwar ta ce mutanen sun rasu ne bayan an kama su bisa zargin haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba, inda MSSN ta nemi Gwamnatin Jihar Neja ta tallafa wa iyalansu, ciki har da biyan Diyya.
MSSN ta kuma nemi a gudanar da cikakken bincike kan mutuwar, wanda zai duba adadin mutanen da aka tsare, yanayin wurin da aka tsare su, samun iska, kulawar lafiya da matakin da jami’an tsaro suka ɗauka lokacin da aka ruwaito cewa mutanen sun shiga mawuyacin hali.
Ƙungiyar ta nemi a bayyana sakamakon binciken ga jama’a tare da ɗaukar mataki kan duk wanda aka samu ya yi sakaci ko wani abin da bai dace ba.
MSSN ta kuma nemi a gaggauta bai wa waɗanda suka tsira kulawar lafiya.
