PP 10
A lokacin ji ya yi ina ma ƙasa ta tsage ya ɓuya a ciki don kunyata. Sarai ya fahimci kamar magana ta faɗa masa sai dai ba yadda ya iya ba ya son Farida ta zargi wani abu dalili kenan da ya tilasta masa jan motar jijiyoyi a sanyaye ya fara tafiya don sauke ta a gida.
Tafe suke tana ta zuba masa hira da ba shi labarin irin rayuwar makaranta da suka yi da Fatima a baya da shaƙuwarsu, amma sam hankalinsa ba ya gun ya na can kan Fatima da tunanin abin da zai iya faruwa bayan ya koma gida don ya san halin kishinta, ta yiwu ma yanzu haka tana can tana kuka, wataƙila ma damuwa ta tayar mata da cutarta.
Ba ya son ya rasa ta haka kuma ba zai iya daina kula ‘yanmata ba musamman biyun nan da suka mallaki abubuwa biyu da yake matuƙar ƙauna ita kuma ta rasa su, ta kuma kasa koya ko don saboda shi.
Khady baby tana da hikimar harshe da iya tsara kalaman soyayya, sam ba ta jin kunyar nuna masa soyayya a gaban ko waye. Farida kuma akwai tsantsar kulawa da kiyaye abubuwan da yake ƙauna sai ta nuna masa ta fi shi ƙaunarsu, daidai da abin shan da ya fi so ta kiyaye har ma takan yi masa tsarabar ire-irensu a duk lokacin da zai haɗu da ita.
Ita kuma Fatimansa ba ta da lura irin wannan, duk tsawon rayuwar aurensu izuwa yanzu ba ta damu da kiyaye wasu abubuwa da yake ƙauna ba ballantana ta yi tunanin faranta masa rai ta hanyar yin su ko samar masa da su shi kuma irin mazan nan ne ‘yan soyayya masu buƙatar tsantsar kulawa.
Farida ta kalle shi da kyau sai ta lura da cewar kwata-kwata hankalinsa ba ya kan hirar da take zuba masa don haka ta ƙura masa ido tsawon sakanni talatin ba ta ga alamar ya fahimci tana kallon shi ba, ga dukkan alamu ma ya zurfafa a kogin tunani hankalinsa ya yi nisa da duniyar zahiri. Ta shiga bubbuga jikin seat ɗin da yake zaune a kai sannu-sannu. Sai da ta yi hakan kamar sau uku ta hanyar ƙara sautin bugawar tata sannan ya yi firgigit ya dawo daga duniyar tunani ya kalle ta da murmushin yaƙe “Me ya faru masoyiya?”
“Kai zan yi wa wannan tambayar na ga ka afka zurfin tunani.”
“Ni ɗin kuma…?” Ta ɗaga gira tare da fitar da sautin “Uhumm!” Daga bakinta alamar tabbatar da zancenta.
Ɗauke idonsa ya yi daga kanta ya mayar kan titi yana ci gaba da tuƙinsa tare da faɗar “Ba abin da kike tunani ba ne.”
Ganin kamar yana kauce-kauce alamar ba ya son amsawa ya saka ta ja bakinta ta garƙame suka fara zaman kurame a motar har ya sauke ta a ƙofar gida, ta jaddada godiyarta tare da yi masa sallama ta shige ciki.
Da hanzari ya juya kan motarsa ya nufi hanyar gida, sai dai yana tafe yana ta saƙe-saƙe da karatun wasiƙar jaki har ya iso gidan. Ba karsashi a tattare da shi ya buɗe gareji ya adana motar sannan ya ƙarasa ciki yana tafiya kamar ba ya son yi.
Bai tsince ta a tsakar gidan ba haka ya ba shi tabbacin tana ɗaki don haka ya shiga da sallamarsa sai dai nan ma ba ta nan. Ya ƙarasa uwar ɗakanta can ma dai duk sammaƙal abin ya fara tsorata shi har yana faɗa a ransa ‘To ko dai ta yi fushi ne ta yi tafiyarta wani gun?’
Falon ya sake fitowa yana ƙoƙarin kiranta a waya sai ga ta nan ta shigo cikin ado mai ɗaukar hankali. Da sakakken baki yake kallonta abin da ya fi ba shi mamaki shi ne yadda ta sauya tufafin jikinta, da dukkan alamu wanka ta sake yi tare da ado na musamman saboda shi. Kujerar zaman mutum ɗaya ya haye ya zuba mata ido kawai, ba baki sai kunne, da ya ga ƙwayar idanunsu ta haɗu zai janye tasa ya yi gefe da ita.
Tun karo shi ta fara yi yana jira ta ƙaraso ya ji da wadda ta zo, zuwa ta yi ta ɗan tsaya nesa da shi kaɗan, “Sannu da zuwa yaya, ya taron?”
Ɗago kansa ya yi don ya ga yanayin da take ciki. Saɓanin abin da ya tsammata sai ya ga tana murmushi mai ɗaukar hankali.
Bai iya buɗe baki ya ba ta amsa ba sai ita ce ta sake cewa “Bari na kawo maka abinci.”
Ba ta jira tamkawarsa ba ta juya zuwa kitchen a nutse ta rungumo kulolin ta kawo ta jere a kan center carpet ɗin in da suka saba zaman cin abinci.
“Abinci ya ƙaraso yaya, Bismillah.” Ta ce da shi tana nuna masa wurin zama. Komawa ya yi tamkar kurma ya yi kamar yadda ta buƙata idonsa na ƙasa ba ya ko son su haɗa ido. Faranti ta ɗauka ta zuba masa lafiyayyen kuskus da ta soya kafin ta fita ta adana masa a kuloli. Abincin sai tiriri yake kamar yanzu aka sauke shi. Ta saka cokali ta ɗebi pepper chicken ta zuba masa a gefe ta tura masa farantin a gabansa.
Ganin ya yi shiru na ‘yan daƙiƙu bai ce komai ba ya sa ta ce da shi “Ka ci abincin mana kar ya huce. Bari na zuba maka lemo.”
Ta aikata kamar yadda ta faɗa sannan ta miƙe ta koma kan kujera tana kallon tv. Sai satar kallonta yake don ya gane yanayin da take ciki, amma duk basirarsa da ƙwarewarsa a ɗago abu da wuri ya kasa gane yanayin da take ciki. Shi dai ya ga fuskarta ba yabo ba fallasa kuma idan za ta yi magana da shi takan yi masa murmushin da yake ƙara jefa shi cikin tsoro.
Tsawon lokaci suka shafe a haka yana ta tsammani ya ji ta yi masa magana kamar yadda ya ga ta fara ɗaukar zafi a mota sai dai shiru kake ji kamar an shuka dusa har dare ba wani bayani. Aka zo kwanciya nan ma ya ji muƙui har ya fara zargin kansa da laifin cutar da ita, duk ya bi ya tsargi kansa ya kasa samun sukuni.
Haka ya kwana da wannan zullumin a ransa yana ta jira ya ga matakin da za ta ɗauka amma shiru har safe ba ta nuna masa wata alamar matsala ba ko a ido kamar ma fatalwarta ce ta kama shi da wannan laifin ba ita ba.
Washegari tun wuraren ƙarfe bakwai na safe ta tashi ta shirya breakfast ta yi wanka ta caɓa adon riga da wando masu kyau da ɗaukar hankali. Riga t-shirt ja mai adon fulawa fara a gaba da farin wando mai ɗigo-ɗigon ja a ciki, sai ta saka hula ja ta yi matuƙar kyau abin ta.
Bayan ta kammala komai ta shirya su inda ya kamata ta koma ciki ta gyara uwar ɗakanta da kuma ɗakinsa ta feffesa turaren ɗaki ta kunna turaren wuta mai daɗin ƙamshi. Cikin ƙanƙanin lokaci gidan ɗakin ya yi fes ko’ina sai tashin ƙamshi yake. Ƙarfe takwas na safe ya fito yin breakfast ta kalle shi ta ga bai yi shirin zuwa aiki ba.
Ta shimfiɗa yanayin mamaki a cikin muryarta “A’ah! Ya na ga ba ka shirya ba, yau ba ka da darusa ne?”
Da abin dai ya ishe shi a zuciya a maimakon ya ba ta amsar tambayarta sai ya ɓige da borin kunya murya sama-sama yake faɗar “Ke Fatima ba na son rayuwar munafunci idan za ki fito ki ce an yi miki laifi ki fito ki faɗa, na kasa gane kanki tun jiya. Me kike shiryawa ne?”
Murmushi ta yi kafin ta ce “Ni ba abin da ka yi mini, ai kowa ya ɓata ya sani wanda kuma ya gyara ma haka.”
Daga wannan furucin ba ta ƙara ce masa kanzil ba ta tashi ta bar masa falon.
Zahirin gaskiya ta ji matuƙar raɗaɗi zuciyarta ta harbu da baƙinciki, duk wannan tarairayar da take yi masa tsakanin jiya da yau tana yi ne kawai don haƙƙi ne a kanta, da kuma neman inda gazawarta take da yake kula wasu ‘yanmatan a waje. Da fari har ta zauna zaman jiran ya dawo a yi ta ta ƙare, can kuma sai ta yi tunanin to meye amfanin hakan? Wani sa’in ai shiru ya fi tafsiri.
Sai ta zaɓi ta bar shi da wahalar yin dogayen tunanuka ya fi ta saka shi yin dogayen maganganu da za su cutar da su duka. Wannan dalilin ya sa ta zaɓi yin shiru da nuna kamar komai bai faru ba da kuma yunƙurin ɗaukar matakin da ta ga ya dace don kuwa ta ji matuƙar baƙinciki a lokacin da ya nuna bai taɓa saninta ba a gaban budurwarsa kuma ƙawarta. Kuma shi ne don rashin ta ido yanzu ya zo yana ƙoƙarin naɗe tabarmar kunyarsa da hauka. A yanzu ta ƙara fahimtar cewa ya fi ciwo da ɗaga hankali mutum ya san an kama shi da laifi kuma a masa shiru kamar ba a sani ba.
‘Wannan sam ba yaya Musana ba ne da muka zuba soyayya lokacin ‘yanmatanci. An sauya mini shi ne ko da ma can haka halinsa yake nisa ce ta yi mini shinge daga munanan ɗabi’unsa? Me na rasa da yake kula wasu ‘yanmatan a waje?’ Ta tambayi kanta tana kifa shi a kan dressing mirrow da take zaune kan kujerarsa ta fashe da kuka mai taɓa rai.
ƁANGAREN SURAYYAH
Abin da Minal ta yi mata ya matuƙar ƙona mata rai, yanzu kuma idan ta ce za ta rama baabarta ta shigo tare mata faɗan don haka ta sunkuya ta ɗauke filonta daga ƙasan ta karkaɗe shi ta juya zuwa ɗakin kakarsu, ban da hmm ba abin da ta ce.
Dube-dube ta fara a ɗakin ta hanyar haska fitila don samun hasken da zai yi mata jagoranci ga ganin abin da take nema.
“Wai me kike nema ne?” Innare ta tambaya.
“Abin da zan shimfiɗa na kwanta nake nema ko da tabarma ce ke ko ma zani in akwai.”
“To kuma yau me ya samu shimfiɗar taku, ko Minal ɗin ba ta fito da ita ba har yanzu?” Tsohuwar ta sake jefa mata tambaya.
Cikin yanayi mai nuna damuwar zuci ta ce “A’a mai katifar ce ta ce ba zan kwanta ba. Kin ga kuwa tun da ba Abbana ne ya sayo ta ba dole na haƙura.”
“Eh! Lallai wuyan Minal ya yi kauri. Ban da fitsara ke ba yayarta ba ce? Abin da ya yi Shu’aibu ai shi ya yi uban nata Aminu. Don ya sayo abu kuwa ai kina da iko da shi. Kodayake biri ko ya karye a ƙugu ba ya fasa hawa rumbu. Bari na je na ji ko uwarta ce ta ɗaure mata ƙugu take yin waɗannan munanan ɗabi’un.” Tayi hanyar fita tana ci gaba da kumfar baki kan cewa ba za a raba mata kan jikoki ba.
Ita dai ba ta daka tasu ba ta ci gaba da neman mafita. Can ta samo tabarmar roba sabuwa dal da ita ta janyo ta tare da ɗaukar wani tsohon bargon Innare da take lulluɓi da shi lokacin sanyi. Tana shirin fita waje kenan wayarta ta yi ƙara alamar kira na shigowa, don haka ta duba sai ta ga baƙuwar lamba. Da kamar ba za ta ɗauka ba sai kuma zuciyarta ta raya mata ta ɗaga mana ai a rashin tayi akan bar arha, ba mamaki abin da zai amfane ta ne.’
Shafa wayar ta yi ta janyo sama ta kashe fitila kana ta ɗaga tare da komawa ta zauna kan gadon jan katako da yake ɗakin tana faɗar. “Wa’alaikumus Salam, barka dai. But sorry don Allah da wa nake magana?”
Ta yi tambayar cikin gatsali tana juya idanuwa don kuwa idan ta ce ba ta san wannan muryar ba ta yi ƙarya mara ma’ana, wannan muryar ko a cikin gigin bacci za ta iya gane ta.
Shi ma a ɓangaren shi ya fahimci kamar gatsalin take yi masa yana da rantsattsen tabbacin ko a taron kasuwa ta ji muryarsa za ta gane shi, hakan da ta yi bai fusata shi ba sai ma murmushin yaƙe da ya yi, mai nema dole ya jure duk wata cin fuska ya yi gwagwarmaya don neman tabbatuwar burinsa. Don haka ya ce “Ayyah! Ba damuwa Amir ne fa.”
“Wane Amir kenan?” Ta sake tambaya da sigar son tabbatar masa da ba ta san shi ba.
Nan ma bai fusata ba ya sake cewa “Amir ɗinki mana, abin ƙaunarki kuma mijinki in sha Allah!”
A ɗan fusace ta ce “Ka ga malam ni ban san wani Amir da kake magana a kai ba, mijina kuma ba kai ba ne in sha Allah.”
Wannan karon kalamanta sun matuƙar soya masa zuciya, duk da zafin rai irin nasa haka ya ci gaba da juriya don kawai ya samu ya ciyo kanta. “Am! Kina jina Surayyah? Don Allah ki daure ki saurare ni ki ba ni ko minti biyar ne a cikin lokacinki mai tsada in samu in yi miki bayanin abin da ya sa na kira.”
Tsaki ta yi kaɗan daidai lokacin Innare ta dawo ɗakin ta kalle ta. “Ke kuma lafiyanki kike tsaki ke kaɗai?” Don sam ita ba ta lura da waya a kunnen Surayyar ba.
Miƙewa ta yi riƙe da kayan da ta riga ta ɗauko suke hannunta ta yi waje tana faɗar “Ina sauraronka. Iya mintuna biyar kawai.”
Daga can gefe inda ba kowa jikin bangon ɗakin kakarsu ta yi shimfiɗarta ta zauna tana ci gaba da sauraron shi.
Ummu Intisar ce
RAUNIN RAYUWA





