Home Daga Marubutanmu KIN TAƁA TAMBAYAR KANKI TA YADDA ZA KI FARANTA WA MIJINKI RAI?

KIN TAƁA TAMBAYAR KANKI TA YADDA ZA KI FARANTA WA MIJINKI RAI?

25
0

Ya ke ‘yar uwa, kin taɓa zama ke kaɗai, kin yi tunani a kan yadda kike tafiyar da zamantakewarki da mijinki? Kin taɓa tambayar kanki cewa: Shin ni mace ce da mijinta yake samun nutsuwa da farin ciki a tare da ita kuwa?

Ɗan dakata!

A matsayinki na matar aure, ba wai dukkan tunaninki ne zai tsaya ne kawai a kan abubuwan da kike son mijinki ya yi miki ba. Ya kamata ki tambayi kanki: Me nake yi domin faranta masa rai? Yaushe ne na ƙarshe da na yi masa wani abu da ya sanya murmushi a fuskarsa? Yaushe ne na ƙarshe da na nuna masa cewa ina alfahari da kasancewarsa a rayuwata?

Ya kamata mace ta fahimci cewa mijinta ma yana buƙatar kulawa, soyayya da kalaman da za su sanyaya masa zuciya. Kada ki ɗauka cewa namiji ba ya buƙatar a kula da shi ko a nuna masa soyayya saboda shi namiji ne.

Ki zama mace mai iya tarbar mijinta da fara’a. Ki kula da tsaftar jikinki da muhalli. Ki riƙa yi masa magana cikin ladabi da biyayya. Ki zama abokiyar shawararsa, wadda zai iya buɗe zuciyarsa ya bayyana damuwarsa a gareki ba tare da tsoron raini ko tozarci ba.

A matsayinki na mace kin taɓa yiwa kanki waɗannan tambayoyin kuwa?

  1. Shin mijinki yana jin daɗin dawowa gida saboda irin tarbar da yake samu daga gare ki?
  2. Shin kina yaba masa idan ya yi abin kirki, ko kuwa kin fi mai da hankali kan kurakuransa na yau da kullum ne?
  3. Shin kina ba shi kulawar da kike son shi ma ya riƙa ba ki?
  4. Shin kalamanki suna ƙara masa ƙarfin gwiwa ne, ko kuwa suna raunana masa zuciya?
  5. Idan mijinki zai bayyana irin rayuwar da yake yi da ke, wane irin abu kike fatan zai faɗa a kanki?

Ya ke ‘yar uwa, kada ki karanta wannan rubutu kawai ki wuce. Ki ɗauki lokaci ki yi tunani a kansa. Ba wai don ki zargi kanki ba, sai don ki gano inda za ki gyara, inda za ki ƙara ƙoƙari da kuma yadda za ki inganta zamantakewarki ta aure.

Ki sani, ba sai an yi babban abu ba kafin a faranta wa masoyi rai. Wani lokaci murmushi, kalma mai daɗi, runguma, addu’a ko kuma nuna godiya kan ƙaramin abu na iya zama babban abin farin ciki.

Ki sake tambayar kanki:
Shin Idan aka tambayi mijinki mene ne ya fi burge shi a tare da ke, wane amsa kike tunanin zai bayar?

#Managarciya

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here