Home Labarai Kano: Kotu ta bayar da belin matar da ake zargi da cizon...

Kano: Kotu ta bayar da belin matar da ake zargi da cizon ɗan sanda tare da yayyaga wa lauya kaya

30
0

Kano: Kotu ta bayar da belin matar da ake zargi da cizon ɗan sanda tare da yayyaga wa lauya kaya

Wata kotun majistire da ke Norman’s Land a cikin birnin Kano ta bayar da belin wata mata mai suna Amina Adamu, wadda ake zargi da cizon wani ɗan sanda tare da yayyage wa lauya tufafinsa.

Rundunar ’yansanda ta gurfanar da Amina a gaban kotun bisa tuhume-tuhume biyu da suka haɗa da kai wa jami’an gwamnati hari da kuma hana ma’aikatan gwamnati gudanar da ayyukansu bisa doka.

A yayin zaman kotun, mai gabatar da ƙara, Lauya Khadija M. Madaki, ta buƙaci a karanta wa wadda ake tuhuma tuhume-tuhumen da ake yi mata.

Bayan an karanta mata tuhume-tuhumen, Amina ta musanta aikata laifukan.

Daga bisani, mai gabatar da ƙarar ta nemi kotun ta ɗage shari’ar domin ba wa ɓangaren masu gabatar da ƙara damar gabatar da shaidu.

Alkalin kotun ya amince da buƙatar, inda ya ɗage shari’ar zuwa ranar 25 ga Nuwamba, 2026, domin ci gaba da sauraron ƙarar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here