Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Ƙofar Kudu a Kano ta fara sauraron ƙarar da aka shigar kan mai shirya fina-finan Hausar nan Abubakar Bashir Mai Shadda, bisa zargin cewa shirin fim ɗinsa na Matan Gida yana ɓata tarbiyya.
Arewa Updates ta rawaito cewa, yayin zaman kotun da Mai Shari’a Ibrahim Sarki Yola ya jagoranta, an saurari bayanan ɓangarorin biyu kan ƙarar da Barista Lawan Muhammad Abdullahi ya shigar.
Mai ƙarar ya yi zargin cewa shirin yana yaɗa abubuwan da suka saɓa wa koyarwar Musulunci da al’adun Hausawa, musamman yadda ya ce ana nuna matan aure da ’yan mata suna neman maza a otal domin samun kuɗi. Ya kuma nemi kotu ta bayar da umarnin gudanar da bincike kan Mai Shadda.
Sai dai lauyan Mai Shadda, Barista Aliyu Usman Hajji, ya bayyana cewa fim ɗin wata hanya ce ta fasaha da ilmantarwa, kuma bai kamata a yanke hukunci a kansa ba tare da kallon cikakken labarinsa ba, kasancewar shiri ne mai dogon zango da zai nuna ƙarshen rayuwar jarumansa.
Lauyan mai ƙara, Yusif Mu’azu Sani, ya nemi a ba su kunshin bayanan kariyar wanda ake ƙara kafin zaman kotu na gaba, inda aka ɗage shari’ar zuwa ranar Juma’a, 18 ga Disamba, 2026, domin ci gaba da sauraro.




