Home Rahoto Sarkin Musulmi ya bayar da umarnin soma duban watan Jumadal Ula

Sarkin Musulmi ya bayar da umarnin soma duban watan Jumadal Ula

16
0

Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya yi kira ga al’ummar musulmi da su fara duban watan Jumadal Ula 1448 daga gobe Lahadi 11 ga Oktoba 2026.

Wannan umarnin yana cikin takardar da Wazirin Sakkwato kuma shugaban kwamitin bayar da shawara kan harkokin addini a masarautar Sarkin Musulmi Farfesa Sambo Wali Junaidu ya sanyawa hannu ya ce a ranar Lahadi 29 ga Rabi’ul-Sani 1448 za a soma duban jinjirin watan Jumadal Ula.

“An buƙaci duk wani musulmi da ya ga watan ya ba da rahoto ga wani basarake na kusa da shi domin sanarda Sarkin Musulmi.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here