Home Rahoto Hukumar Hisbah ta kai samame a Otal-Otal 8 a birnin Sakkwato

Hukumar Hisbah ta kai samame a Otal-Otal 8 a birnin Sakkwato

24
0

Hukumar Hisbah ta Jihar Sokoto ta kai ziyarar ba-zata otal-otal takwas a birnin Sokoto a ranar Talata, 28 ga Yuli 2026.

Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Hukumar Hisbah ta Jihar Sokoto ta fitar.

Kwamandan hukumar, Malam Usman Abdullahi Jatau, ne ya jagoranci ziyarar.

Otal-otal ɗin da suka ziyarta sun haɗa da Karma Guest Inn, Giginya Hotel, Sokoto Guest Inn, Dan Kani Guest Inn, Soul Care Hotel, Grand Ibro Hotel, Triple C Plus Guest Inn da Options X Luxury Hotel.

Hisbah ta danganta ziyarar da tabbatar da cewa otal-otal ɗin suna gudanar da ayyukansu bisa doka da ƙa’idoji.

Ba a ba da bayanin kame a wannan ziyarar ba ana danganta zuwan da yinƙurin samun fahimtar juna tsakanin masu kula da wuraren da hukumar don ganin an tsaftace jihar daga aiyukkan baɗala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here