Home Rahoto ‘Yan sanda sun tabbatar da sace Malamai 6 da suka je taron...

‘Yan sanda sun tabbatar da sace Malamai 6 da suka je taron siyasa a gidan Sanata Yari a Zamfara 

19
0

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu Malamai guda shidda da suka je taron siyasa a gidan shugaban yekuwar sake zaɓen Tinubu a karo na biyu Sanata Abdul’aziz Yari dake ƙaramar hukumar Talatar Mafara a Zamfara.

Malaman da suka fito a ƙananan hukumomin Bakura da Takarar Mafara su ne Liman Yahuza first Jumma’at Dogon Maɗacci da Magawata Abdullahi second Jummaat Dogon Maɗacci da Malam Shehu Dakko da  Liman Bala Fagon da Na’ibi Tasi’u Tungar Nagudai, da wani ɗayan da ba a gane sunansa ba.

A wani bayani da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Zamfara DSP Yazid Abubakar ya fitar ya tabbatar da yin garkuwa da Limaman su shidda, “rundunar ‘yan sanda ta shirya dawo da limaman da aka sace su shidda kan hanyar Dakko-Damri a yankin Bakura.

“Lamari da ya faru ranar Assabar in da ‘yan bindigar ɗauke da miyagun makamai suka tare motar da ta ɗauko waɗanda aka sacen dukkan su shidda limamai ne sun yi tafiya zuwa Talatar Mafara a hanyar dawowa ne aka yi garkuwa da su.”

Ya ce jami’an tsaro suna kan sintiri da bincike a daji domin ganin sun dawowa da waɗanda aka sacen a kuma hukunta ɓatagarin da ke wannan halin.

Malaman sun tafi taro ne kan harkokin siyasa a gidan Yari donin neman goyon baya ga tafiyar shugaban ƙasa Tinubu bayan kammala taron ne da  suka tafi wannan matsalar ta rutsa da su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here