Home Daga Marubutanmu ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 46

ƘADDARA TA RIGA FATA: Fita Ta 46

17
0

NA MARUBUCIYA:-
AUNTY NICE
@wattpad AuntyNice.

SADAUKARWA GA ƳAƳA NA HASKEN ZUCIYA TA:-
NABEELAH ARABI
NUHU ARABI

SHAFI NA 46

_______ Uncle Abdallah kuma da Abba ganin nida su Ummi duk mun suma a wurin sai sukaji hankalinsu yayi matuƙar tashi, jiki na ɓari Abba ya ƙira number Dr su, shi kuma Uncle Abdallah yadda kasan tsohon soja haka jikin shi yake rawa, daga ya dubi Aisha sai yaji kaman yayi ta ihu don tsananin tausayinta da shiga tashin hankali, a zuciyar shi kuma yana ayyana duk wanda yake da hannu a cikin raping ɗin Aisha da akayi wallahi bazai barshi ya sarara ba.

Dr su biyu suka zo, da yake Daddy ya gaya mishi case ɗin, zuwan su gaba ɗaya suka fara aikin ceto rayuwar mu, babu ɓata lokaci nida Aunty hauwa muka farfaɗo, amma Ummi dole suka ɗauketa akayi mota da ita, muna tashi daga ni har Aunty hauwa da gudu mukayi wurin Aisha, zuwa lokacin naga an rufe mata jikinta da bedsheet, ba kaman zuwan mu tana kwance haihuwar uwarta ba, rungumeta Aunty hauwa tayi tana kuka kamar ranta zai fita, nima haka na haɗasu na rungume ina tayata kukan, da ƙyar Uncle Abdallah ya sa muka sake ta, shi ya ɗauketa mukayi hanyar zuwa asibitin Dr Basheer, wato CITY CLINIC da yake wannan asibitin su Ummi suke zuwa, muna zuwa asalin babban likitan wato Dr Basheer yayi kan Aisha shi da wasu nurses guda 2, ita kuma Ummi ɗayan Dr sani ya rufu akanta.

Ni dai ranan na koma kaman mace, kafaɗan Aunty hauwa kawai na kwantar da kai na sai kuka muke ta rerawa nida ita, daga Abba har Uncle Abdallah kallon mu sukeyi ba tare da sun iya furta komai ba, gaba ɗaya kansu suke ji ya kulle, waye zai shigo har cikin gidan ya iya wucewa har ɗakin Aisha yayi mata wannan mummunan illar ba’a ganshi ba? Gaskiya abun yayi matuƙar ɗaure musu kai, kawai sunyi shiru ne suna jiran farfaɗowar Aisha da Ummi ne kawai, sai su shiga bincike.

Ummi bata daɗe ba ta farfaɗo, amma Aisha sai da tayi rabin awa tukun ta farfaɗo, hakan ma tana farfaɗowa suka mata alluran kashe zafi don su samu su mata ɗinkin wurin, domin ba ƙaramin jin ciwo tayi ba, bayan an gama komai su Abba suka bi Dr basheer har cikin office ɗin shi, inda yayi musu bayanin BPn Ummi yayi mummunan hawa, ya kamata a kiyaye abinda zai dinga tayar musu hankali, sannan case ɗin Aisha kuma yayi musu jajen abinda ya faru, sannan ya ce su neme police a cikin case ɗin, don ma abinda ya kamata suyi ne tun farko, wato saida police tukun ya karɓi Aisha, a haka muka wuce zuwa ɗakin da Ummi take kwance idonta a rufe kaman mai bacci, amma kuma ba baccin ta keji ba, kawai tana sauraren kukan da Aunty Hauwa ta keyi ne, wanda ta kejin shi kaman zai fasa mata heart ɗinta.

Gefen Aunty hauwa Uncle Abdallah ya zauna yana ta rarrashinta, yana kuma roƙonta da ta je wurin Aishan ta zauna da ita, shi kuma Abba zuwa yayi ya riƙe hannun Ummi, wanda tana jin zuwan shi inda ta ke ta buɗe idon ta a hankali , ƙurawa Abba ido tayi nata idon ma ya fara zubar da hawaye.

“kiyi haƙuri Fatima, insha Allahu yanzu zamuje mu miƙawa police case ɗin, kuma ina da tabbacin zasu gano wanda ya shiga har gidan ya aikata wannan mummunan aikin wa Doughter, insha Allahu zamu bi mata hakkin ta”, Abba ya faɗa yana jijjiga kan shi alaman abinda yake faɗa babu fashi, hannu Ummi ta miƙo mishi ya ɗaga ta, zama tayi fuskanta ɗauke da wani irin ƙunci, amma sai da tayi ɗan murmushi kaɗan, ido ta ƙurawa Aunty hauwa na zuwa wani lokaci, sannan ta dawo da kallonta kaina da nake tsaye a bakin ƙofan ɗakin tun shigowan mu ina kuka a tsaye a wurin, sannan ta karkaɗa kanta, ta dawo da kallonta kan Abba, hannuta ta ɗaga ta ɗaura a kan saitin zuciyarta, “Abba wani police zaku nema akan wanda yayi fyaɗe wa ƴata? Bayan wanda ya aikata yana cikin gidan da kuke?” runtse ido ta sakeyi hawaye yana zuba a fuskanta da gudun gaske.

Da sauri Abba ya dubeta yace, “ban gane me kike faɗa ba Fatima? Kina nufin kinga shigowan wani ne cikin gidan, ko kuma me kike nufi”? Ya faɗa gaba ɗaya hankalin shi a tashe.

“Abban su kana tunanin akwai wani daban da zai aikata wannan mummunan aikin bayan ɗanmu Hassan? Tabbas Hassan shi ne yau ya saka hawaye mai zafi da ƙunan xuciyar da bamu san ranan ƙarshen shi ba a rayuwar mu, Hassan yau shi yasaka na kejin kunyar duban idon Abdallah da Hauwa, yake sani jin da wani idon zan dubi Baban Narabi, yayah zanji ranan da Allah ya haɗani da Baba Umar yaji irin saken da nayi na riƙon amanan da ya bani?” kuka Ummi ta saka mai ƙarfin gaske, wanda daga ni har Aunty hauwa ma kukan mu keyi, jiki na rawa Abba ya sake buɗe baki yace.

“Fatima ban fahimci me kike nufi ba, shin kinga Hassan ya shiga ɗakin ta ne? Don Allah ki fahimtar dani Fatima, komai ya kulle mun”, ya faɗa kaman shima raunin shi zai saka shi zubar da hawayen.

Juyawa Ummi tayi ta dubi kowa da yake cikin ɗakin, sannan ta dubi Abba tace, “gamu nan dukkan mu a hallare a ɗakin, shi kaga Hassan a cikin mu? Baka tunanin mai ya hana shi zuwa inda muke? Wallahi jikina ya bani Hassan ne ya aikata wannan mummunan illar wa rayuwar Aisha, domin yayi katanga wa ɗan’uwan shi na auren Aisha, shi kuma a bashi aurenta, kuma nayi alƙawari idan har nono na Hassan ya sha tou na haramta mishi auren Aisha har abada”.

Waya da sauri Abba ya ɗauko ya shiga dialing number Hassan, wanda dukka layin shin a rufe suke, haka Abba ya ajiye wayan shi jiki a sanyaye, ɗago idon shi yayi ya dubi uncle Abdallah yace, “muje mu miƙa case ɗin zargin Hassan da mukeyi a wurin police” Abba ya faɗa jikin shi yana ta rawa, wani zufah mai azaban zafi yana karyo mishi.

Murmushi Uncle Abdallah yayi ya matsar da Aunty hauwa dake lafe a jikinshi ya ƙaraso inda Abba yake, hannu ya dafa a kafaɗan shi yace, “haba Yayah! Kana ganin ni da kaina zan iya shari’a da ɗana ne akan ƴata? Wallahi Allah ya sauwaƙa, nasan koda Baba Umar yana raye bayida abinda zaiyi sama da addu’a da haƙuri, ae Hassan ɗan mune, kuma idan ba rashin godiyar Allah irin namu ba, ta yayah zamuyi shari’a da kai? Don kuwa yin shari’a da Hassan tamkar da kai mukayi, wannan abun mun ɗauke shi a ƙaddaran rayuwar Aisha, kuma wannan shine ƘADDARA TA RIGA FATA munyi fatan haɗa aure tsakanin Hussain da Aisha, amma ƙaddaran da ta gifta tsakanin Hassan da Aisha ta saka dole mu haƙura mubar Hassan ya auri Aisha, mudai fatan mu Allah ya bata sauƙi, don ni tun ganin Aisha ban zargi kowa ba sai Hassan, saboda irin kalaman shi da yayi tayi a daren jiya, dama duk hankalina bai kwanta ba, Allah-Allah nake gari ya waye muje Narabi akan maganan auren Hussain da Aisha, toh amma ga abinda Allah ya aiko mana, dole muyi haƙuri”.

“Idan kai kanaga ka haƙura tou ni ban haƙura ba, dole sai nayi shari’a da Hassan, kuma babu abinda zai hana auren Aisha da Hussain, don abinda yayi bai isa yasa mu chanja ra’ayin mu ba, nayi rantsuwa koda mazan duniya sun ƙare tou har abada Aisha bazata taɓa auren Hassan ba, sharrin shi ya koma kanshi”, Abba ya faɗa yana miƙewa don tafiya wurin police.

Uncle ne ya ɗauki waya ya ƙira Baban Narabi, a handsfree ya saka, sannan yayi sallama ya gaida Baban, murya a raunane ya shiga zayyanawa Baban abinda yake faruwa, a ɗaya ɓangaren kuma sai, “innalillahi wa’innah ilahir raji’un” Baba yake ta maimaitawa, bayan Uncle ya gama gayawa Baban komai, sai Baban yace ya bashi Abba, nan Uncle ya gaya mishi wayar tana handsfree kowa yana jin shi, gyaran murya Baba yayi sannan yace.

“Gambo! Wallahi kaji Allah ɗaya yake ko? Toh idan ka fitar da wannan magana waje har wani daban ma yaji, toh ban yafe maka ba duniya da lahira, daga kai har Fatima sai nayi shari’a daku agaban ubangiji, kuma ban yafewa duk wanda yayi mummunan furuci wa Hassan ba tsakanin kai da Fatima ba, mu ƴan halal ne ba butulu ba, munyi imani da ƙaddara mai kyau da marar kyau, shin idan ɓarawo ne ya shigo gidan yayi mata haka yayah zakuji? Hassan fa mun sanshi mun san kuma shaiɗan ne yafi ƙarfin zuciyar shi ya saka ya aikata mata haka bawai don halin shi bane, saboda haka kubar maganan mun yafe duniya da lahira, kuma Aisha tana gama istibira’i za a yi auren su da Hassan ɗin”, Baban Narabi ya ƙarasa maganan cikin dakiyar zuciya, ina jin su nayi sauri na runtse ido na, amma jin muryan Ummi da maganan da ta keyi cikin kuka ya saka ni buɗe ido na ƙura mata shi.

“Baba don Allah kayi mun rai, wallahi Hassan idan ya auri Aisha bazan iya rayuwa ba, duk ranan da aka aura mishi Aisha ranan ni kuma zan koma ga ubangiji na Baba Hussain na amince ya auri Aisha, idan muka bawa Hassan zai ga kaman yayi nasara ne akanmu, kuma Hassan bai da halin kirkin da zai riƙe mun ɗiyata cikin mutunci, tunda baiji tausayinta ba ya aikata mata haka, baiji tausayin wani hali mu iyayen shi da ɗan’uwan shi zamu ji ba ya aikata mana wannan mummunan aikin ba, toh bazai samu abinda yake so ba cikin sauƙi, Baba tunda kace baka yafe ba idan munyi shari’a da shi ba ko kuma muka bishi da mummunan fata ba, tou Baba muma kamana adalci mu samu sauƙi a zuciyar mu, ka amince babu aure tsakanin Aisha da Hassan har abada”, Ummi ta ƙarashe tana fashewa da kukan da ban taɓa gani tayi irin shi ba.

Da gudu Aunty hauwa ta ƙarisa jikinta ta rungume ta ƙam a jikinta itama tana kukan gaske, murmushi Baban Narabi yayi cikin ƙarfin hali yace, “naji Fatima Allah ya muku albarka, ya baku haƙurin jure wannan babban damuwan a zuciyar ku, na amince kubawa shi Hussain ɗin idan bazai damu ba”, sannan ya musu sallama ya ajiye wayan.

Aisha ba ita ta samu kanta ba sai da tayi sati biyu a asibitin, bayan an sallame mu mun koma gida ne, sai uncle Auwal ya zo tare da Hassan wanda gaba ɗaya duk yabi ya lalace, duk yadda uncle auwal yayi Ummi ta daina kuka da ta ga Hassan amma kasawa tayi, dole saida Mama tazo daga Misau suka haɗu akayita kwantar mata da hankali, da ƙyar ta amince shima da sharaɗin ba zai sake shigo mata side ɗinta ba, ba yadda aka so ba aka amince, ita kuma Aunty hauwa bayan sati ɗaya suka wuce da uncle Abdallah, haka gidan ya dawo shiru babu daɗi, nine ma dole nake zuwa parlourn Ummi nake ta yata ɗan hira, wanda gaba ɗaya Ummi ta kasa samun lafiya, bata kwana biyu bata kwanta BPn ta ya hau ba, ita kuma Aisha gaba ɗaya ma bata fitowa parlour, kullum tana ɗaki tare da Umma da aka ɗauko ta daga misau suna kwana tare, kuma hakan wataran Umman zata zo tayita yiwa Ummi faɗan yadda ta hana kanta saƙat.

Shi kuma Hassan idan mun haɗu da safe da ƙyar yake iya ɗaga ido mu gaisa, nima kuma sai ina jin shi kaman wani baƙo, bana iya sakewa kuma da shi.

A haka lokaci yayita tafiya har Aisha ta cika wata uku da faruwan abin, wanda zan iya cewa baifi sau 2 na taɓa ganin ta ba tunda abin ya faru, ana saura kwana uku ta cika wata ukun na ganta tana fitowa a ɗakin Ummi da bata da lafiya tana kwance, ni kuma zan shiga duba jikin Ummin, gaba ɗaya sai danaji zuciyana ya yanke, domin wani irin rama da Aisha tayi babu komai fuskarta sai karan hanci, muna haɗa ido tayi sauri ta sunkuyar da kanta, bata iya ce mun komai ba ta ratsa ta gefe na ta wuce, haka na bita da kallon cike da tausayinta.

Ina shiga ɗakin Ummi kuma na samu Umma sai faɗa take tayi mata akan ta daina yawan zama tana wannan kukan, kallon Ummi nayi ganin yadda duk itama ta rame ta fita hayyacin ta kawai sai naji kuka ya zo mun, gaskiya Hassan ya wargaza mana duk wani farin ciki na zuri’ar mu, don Aunty hauwa kullum mukayi waya don taji jikin Ummi, kawai kuka zakaji tana yi, wanda ni nakasa fahimtar meye matsalan Aunty hauwa, halin da aka jefa ƴarta ce yake da munta ko kuma halin da Ummi take ciki ne damuwan ta?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here