Home Rahoto Gwamnatin Kano ta Umarci duk Ma’aikacin da ya samu albashi Yuli sau...

Gwamnatin Kano ta Umarci duk Ma’aikacin da ya samu albashi Yuli sau biyu ya mayar da daya

20
0

Ana zargin Kwayar Cuta ta shiga babban Asusun biyan Albashin ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kano inda aka turawa wasu ma’aikata albashi sau biyu a lokacin guda.
Gwamnatin Jihar Kano ta umarci ma’aikatan gwamnati da aka tura musu albashin watan Yulin 2026 sau biyu su gaggauta mayar da kuɗin da suka karɓa fiye da kima cikin asusun gwamnatin da ake biyan albashi.
A cikin wata sanarwa da Ofishin Akanta Janar na Jihar Kano ya fitar, gwamnatin ta bayyana cewa wata matsala ta samu a tsarin biyan albashi, lamarin da ya sa wasu ma’aikata suka karɓi albashin watan Yuli sau biyu a lokaci guda.
Sanarwar ta ce bankin da abin ya shafa ya yi ƙoƙarin dawo da kuɗaɗen da aka tura bisa kuskure, amma hakan bai yi nasara ba.
Saboda haka, an buƙaci duk ma’aikatan da abin ya shafa su mayar da kuɗin cikin Kano State E-Salary Account na gwamnatin jihar.
Haka kuma, gwamnatin ta umarci ma’aikatan da su kai shaidar biyan kuɗin zuwa Ofishin Akanta Janar da ke kan titin Commissioner Road a Kano domin tantancewa da kuma ba su takardar karɓar kuɗi ta hukuma.
Gwamnatin ta jaddada cewa tana sa ran cikakken haɗin kai daga ma’aikata wajen mayar da kuɗaɗen domin tabbatar da gaskiya da riƙon amana wajen kula da kuɗaɗen jama’a.
Mikiya Hausa ta lura cewa sanarwar ba ta bayyana takamaiman abin da ya jawo wannan matsalar ba, sai dai ta tabbatar da cewa wasu ma’aikata sun karɓi albashin watan Yuli sau biyu, kuma ana buƙatar su dawo da kuɗin da suka karɓa fiye da haƙƙinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here