Home Labarai ‘Yan bindiga sun kutsa masallaci sun kashe mutane a Sokoto

‘Yan bindiga sun kutsa masallaci sun kashe mutane a Sokoto

46
0

Akalla mutum bakwai ne suka rasa rayukansu yayin da ’yan bindiga suka kai hari kauyen Tsamaye da ke Karamar Hukumar Sabon Birni, inda suka kashe wasu a cikin masallaci tare da yin garkuwa da mazauna yankin.

’Yan bindiga sun kashe masallata bakwai tare da yin garkuwa da wasu mutane a ƙauyen Tsamaye na Jihar Sokoto.

Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin sanarwar da ƙungiyar kare haƙƙin bilʼadama ta Amnesty International ta fitar a ranar Laraba, 29 ga Yuli 2026.

Maharan sun kai harin masallacin ne da sanyin safiya a ƙauyen Tsamaye na Ƙaramar Hukumar Sabon Birni, inda suka yi garkuwa da mutane da ba a bayyana adadinsu ba.

Amnesty International ta nuna cewa mata da ƙananan yara suna cikin waɗanda aka yi garkuwa da su.

Ƙungiyar ta kuma bayyana cewa tun daga Janairun 2026 ’yan bindiga sun kai hare-hare da dama a ƙauyukan Sabon Birni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here