Home Rahoto Za mu cigaba da ƙarfafa haɗin kai da samar da abin dogaro...

Za mu cigaba da ƙarfafa haɗin kai da samar da abin dogaro ga mata a Sokoto—-Barista Sa’adatu Yanusa

14
0



Mai baiwa Gwamnan Sakkwato shawara kan rage raɗaɗin talauci, Kodineta tafiyar City Boys ta jiha   Barista Sa’adatu Yanusa Muhammad ta ƙaddamar da shugabannin mata a yankuna uku da kananan hukumomi 23 na jihar Sakkwato.


 Ƙaddamarwar da aka yi a Otal na Karma cikin birnin jiha wanda Kodinetan ta yi a wurin bukin ta bayyana haɗuwar haɗaka ce da za ta samar da manufar haɗin kai da za ta haifar da nasara a wannan(City Boys) tafiyar a dukkan faɗin jihar Sakkwato. 


Ta fahimci taron bai tsaya kawai kan shugabanci ba har da ƙarin ƙarfi don samar da sakamako mai kyau a ƙananan hukumomin jihar.
“Mata suna da rawar da za su taka don tabbatar da tafiyar ta shiga lungu da saƙo, dole ne mu taimaki junanmu, mu ƙarfafa haɗin kai, da zaburar da mutane su shigo a yi da su a cikin tarbiya da hangen nesa.”


“Wannan tafiyar za ta tsaya kai da fata wurin ganin mata sun samu cigaba ta hanyar samar musu abubuwan dogaro da kai, don tabbatar da kare mutuncinsu a cikin al’umma,” a cewar Barista Sa’adatu.


Mataimakiyar darakta kan harkokin mata a tafiyar Hajiya Shafa’atu Sanusi Tukur Faru a jawabin godiya ta nuna farin cikinta da godiya ga duk waɗanda suka halarci taron da ganin an yi nasara kan ƙaddamarwar.


Shafa’atu ta ce ƙungiyar ta samu cigaba ne kan goyon baya da zaburarwar da shugabanni ke yi, musamman Barista Sa’adatu sadaukarwa da samar da harkokin dogaro da kai ga mata da take yi ya taimaka wurin samun haɗin kai a tsakanin mambobin ƙungiya.


“Wannan tafiyar da muka fara, muna roƙon Allah hikima da haɗin kai da nasara a dukkan harkokinmu.”


Tana fatan tafiyar City Boy ta cigaba da samun nasara da ƙarfi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here