Home Labarai Dakta Gumi ya shawarci Shaikh Jingir da ya cire addini daga siyasar...

Dakta Gumi ya shawarci Shaikh Jingir da ya cire addini daga siyasar jam’iyya

3
0

Malamin addinin Musulunci, Dakta Ahmad Gummi, ya yi kira da a nisantar da addini daga siyasar jam’iyyu, yana mai cewa bai kamata a jawo batun addini cikin fafatawar siyasa a Nijeriya ba.

Kiran na Gumi na zuwa ne bayan Sheikh Sani Yahaya Jingir ya goyi bayan tikitin Musulmi da Musulmi na APC, tare da kira ga Musulmai su zaɓi Shugaba Bola Ahmed Tinubu, in da yake ganin zaɓensa a matsayin wani aiki na musulunci.

Da yawan mutane na ganin APC sun samar da tsarin ne domin mafitar tafiyarsu ba don a waƙilci musulunci ba.

Shaikh Jingir nada damar tallata wanda yake so amma ba bisa doron addini ba sai don gamsuwa da tafiyar, kuma da yawan mutane na ganin kuskuren shigar da addini a wurin da ba addinin ake nufi ba.

A gefe guda, Sanata Rabi’u Kwankwaso ya ja kunnen jingir kan ya riƙe mutuncinsa ya daina sanya kansa a lamarin siyasar jam’iyya, in har da gaske yake marawa maganar Muslim muslim tau ya yi kira da shugaba Tinubu ya fara daga gidansa, a ga ya yi Muslim muslim(shi musulmi matarsa ma musulma).

Ya yi kira ga harkar siyasa ta jam’iyya ta zama ta masu ita saɓanin goyon bayan abin da yake da kuskure a ciki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here