Home Siyasa PDP na son Ɗanjumma Goje ya zo ya yi takarar Sanata don...

PDP na son Ɗanjumma Goje ya zo ya yi takarar Sanata don ya ƙarawa Pantami ƙarfi

19
0

Jam’iyyar PDP a jihar Gombe ta yi wa Goje tayin tikitin takarar Sanata domin taimaka wa Pantami

Tsohon Gwamnan Gombe, Sanata Muhammad Danjuma Goje, na fuskantar matsin lamba da ya fice daga APC ya koma PDP domin ya mara wa ɗan takarar gwamnan jam’iyyar, Farfesa Ali Isa Pantami, baya a zaɓen 2027.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito tsohon Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo da Pantami na ƙoƙarin shawo kan Goje ya koma PDP, ganin cewa APC ba ta ba shi tikitin komawa Majalisar Dattawa ba.

Goje, wanda ke da magoya baya a dukkan mazabun sanatan Gombe, na tattaunawa da PDP kan yiwuwar komawarsa jam’iyyar. Haka kuma, ADC na daga cikin jam’iyyun da ake cewa suna neman goyon bayansa kafin zaɓen 2027.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here