Home Rahoto Sojoji sun tarwatsa ‘yan bindiga kan iyakar Zamfara da Kebbi

Sojoji sun tarwatsa ‘yan bindiga kan iyakar Zamfara da Kebbi

3
0

Rundunar Sojin Saman ƙasarnan ta kai hari ta sama kan ’yan bindiga kimanin 240 da suka taso daga Jihar Zamfara zuwa Makuku da ke Jihar Kebbi, inda suka hallaka da dama daga cikinsu.

Arewa Updates ta rawaito cewa, wannan na cikin bayanin da Mai taimakawa Gwamnan Jihar Zamfara kan Sabbin Kafofin Yaɗa Labarai, Mugira Yusuf, ya fitar.

Ya ce, an kai harin ne ranar Litinin 10 ga Agusta, 2026, yayin da ’yan bindigar ke kan hanyar kutsawa cikin wasu al’ummomin Jihar Kebbi.

Sanarwar ta ce, Samamen ya tarwatsa shirin kutsensu tare da hallaka da dama daga cikin waɗanda ke cikin gungun.

Ya ce, Rundunar Sojin ƙasa da ’yan sanda na ci gaba da aikin dakile sauran ’yan bindigar da suka tsere, yayin da ake ci gaba da tantance ainihin adadin waɗanda aka kashe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here