Home Rahoto Tinubu zai sake karɓo bashin dala miliyan $516 don cigaba da gina...

Tinubu zai sake karɓo bashin dala miliyan $516 don cigaba da gina hanya a Arewa

11
0

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aika da wasiƙa ga Majalisar Dattawa yana neman amincewarta domin karɓo sabon rancen kuɗi na dala miliyan $516.

Rahotanni sun nuna cewa za a yi amfani da kuɗin wajen aiwatar da manyan ayyukan ci gaba, ciki har da gina manyan hanyoyi da sauran muhimman abubuwan more rayuwa a ƙasar.

An kuma bayyana cewa tuni Majalisar ta miƙa wannan buƙata ga kwamitin da ke kula da basussuka domin nazari cikin gaggawa.

Daga cikin abin da za a yi da bashin akwai cigaba da hanya da ake yi daga Sokoto zuwa Lagos.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here