Home Siyasa Shari’ar da ake yi wa Abubakar Malami ba za ta hana shi...

Shari’ar da ake yi wa Abubakar Malami ba za ta hana shi ci gaba da neman takara Gwamna ba – ADC

19
0

Jam’iyyar ADC a jihar Kebbi ta ce shari’ar da ake yi wa tsohon Ministan Shari’a kuma tsohon Antoni-Janar a zamanin mulkin Buhari, Abubakar Malami, SAN, tana da nasaba da siyasa, kuma ba za ta hana shi ci gaba da shirye-shiryen neman takarar zaben 2027 ba.

Jam’iyyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar bayan taron shugabanninta a Sokoto, inda ta jaddada cewa za ta ci gaba da mayar da hankali wajen kokarin kayar da jam’iyyar APC mai mulki a babban zaben 2027.

ADC ya nuna gamsuwa cewa Malami zai iya kayar da APC a zaɓen 2027 saboda karɓuwar da ya samu a tsakanin mutanen jihar Kebbi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here