A ƙalla mutum 13 ne ‘yan bindiga suka kashe a wani sabon hari da suka kai a ƙaramar hukumar Sabon Birni jihar Sakkwato, duk da jami’an tsaro sun kai ɗauki har sun daƙile kaiwa wani ƙauye hari.
Farmaki wanda ya faru a tsakanin daren Alhamis zuwa safiyar Juma’a ya yi sanadin rasuwar mutum shidda a ƙauyen Mazau, huɗu Turtsawa sai mata biyu da wasu manoma uku a ƙauyen Tsamaye.
Mutanen garin sun ce ‘yan bindigar sun yi ƙudirin zagaye unguwar Lalle da marecen Alhamis, ɗaukin jami’an tsaro da ‘yan banga in da aka shafe awowi ana bata kashi ne ya sa burinsu bai cika ba.
Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya ce maharan ba su sha da daɗi ba bayan da jami’an tsaro suka galabaita su.
“Sojoji da ‘yan banga sun fuskance su da gaskiya in da aka ɗauki awowi ana musayar wuta, tabbas ‘yan bindigar sun sha wuya an samu jikkata nasu amma sun kwashe matattunsu sun tafi da su domin haka suke yi,” a cewar mutumin.
A cewarsa bayan sun kasa shiga Unguwar Lalle shi ne suka dawo Mazau suka kashe mutum shidda, kafin su tafi Turtsawa in da suka kashe huɗu tare wasu mata biyu.
Majiyar ta ce maharan sun dawo da safiya Jumu’a suka kashe manoma uku suna kan hanyarsu ta zuwa gona a ƙauyen Tsamaye.
“Sun yi aniyar sake farmakar mu da safen da muna janazar mutanen sojojin ne suka kore su.”
Ɗaya daga cikin jagorori a Sabon Birni ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce wannnan na cikin matsin da ‘yan bindiga ke yi a yankin.
Ya ce a ranar Laraba ‘yan bindigar sun yi garkuwa da mutane uku manoma a Sabon Birni.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Sakkwato DSP Ahmad Rufa’i ya ce har yanzu bai karɓi rahoton abin da ya faru ba a yankin.





