‘Yan bindiga sun keshe ‘yan gudun hijira uku sun yi garkuwa da wani a kauyen Gangara cikin karamar hukumar Sabon Birni jihar Sakkwato.Wadanda aka kashen suna cikin ‘yan gudun hijirar da suka bar kauyensu domin ya zama kufai, don su rika samun abinci ganin an kyale su can ana ta kai masu farmaki.’Yan gudun hijirar suna a garin Sabon Birni da Isa amma saboda wahala sun sake komawa kauyensu.Daya daga cikinsu ya sanar da wakilinmu su kusan 200 suka koma kauyen nasu na Gangara a ranar Laraba data gabata, ashe ‘yan bindigar suna a wuraren sun boye a nan ne suka buda masu wuta.Ya ce a lokacin da suna tsalkar gulbin na kusa da kauyensu ne ‘yan bindigar suka farmake su hakan ya da yawa wasu sun gudu.”Mutum uku sun mutu a lokacin da suke yunkuin tsallako gulbin, a ruwan suka fadi ya kuma tafi da su ba gawar da aka dauko a gulbin.”Margayan sun hada da Hurera Halilu uwa ce da ta bar yara bakwai, da Hassan Haruna da Sani Musa.Majiyar ta ce haka kuma ‘yan bindigar sun yi garkuwa da Muhammad Malam Bakwai.Ya ce ‘yan gudun hijirar ba su so dawowa kauyen ba, saboda dan bindigar nan Kacalla Jamau Baki da ke da kawance da Bello Turji an ce ya fadi duk wanda ya samu a kauyen nan sai ya kashe shi.Shugabannin kauyen sun soki gwamnati kan ba wani taimako da gudunmuwa da suke kai masu hasalima ba wani jami’in gwamnati da ya ziyarce su.Duk yunkurin jin tabakin rundunar ‘yan sandan jiha bai yi nasara ba, saboda jami’in hulda da jama’a DSP Ahmad Rufa’i bai kusa ga waya a lokacin da aka kira da tura masa sakon kar takwana.





