Ta Lallaba Saudiyya, Tana So a Taimaka wa Najeriya kan Karatun Allo
Uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta buƙaci Masarautar Saudiyya ta haɗa hannu da Najeriya wajen gyara tsarin ilimin allo da kuma yaran da ba sa zuwa makaranta. Ta ce rashin bai wa waɗannan rukunin yara ilimi na zamani na iya zama babbar barazana ga tsaron ƙasa
Uwargidan shugaban ƙasar ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da ta karɓi jakadan Masarautar Saudiyya a Najeriya, Yousef Mohammed Al-Balawi, a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, in ji rahoton Punch.
A cikin wata sanarwa da babbar mataimakiya ta musamman kan harkokin yaɗa labarai ga uwargidan shugaban ƙasa, Busola Kukoyi, ta fitar, an bayyana cewa Oluremi Tinubu ta nemi haɗin gwiwar Saudiyya wajen taimaka wa yaran Almajirai.
A cewarta, haɗin gwiwar zai mayar da hankali ne kan haɗa koyarwar Larabci da addinin Musulunci da kuma ilimin boko.
Ta ce wannan tsarin ya dace da tsarin Almajiranci, wanda ya ta’allaka ne kan koyar da Alƙur’ani amma bai cika haɗuwa da ilimin zamani ko koyon sana’o’i ba.
Ta ce: “Ina aiki tare da mata da yara marasa galihu a cikin al’umma. Ina matuƙar tausaya wa yaran Almajirai da ke Arewacin Najeriya.
Ina ganin suna buƙatar kulawa ta musamman. “Yawancin matsalolin tsaro da ake fama da su a ƙasar nan, idan ba a kula da irin waɗannan yara ba, ban san abin da zai faru nan gaba ba.






