Home Kiyon Lafiya Tsadar Magani ita ce babbar wahala a kula da ciyon tabin qwaqwalwa

Tsadar Magani ita ce babbar wahala a kula da ciyon tabin qwaqwalwa

15
0

Tsadar Magani ita ce babbar wahala a kula da ciyon tabin qwaqwalwa

Cutar ciyon tavin hankali ciyo ne da yake addabar mutane a kowace nahiya ta Duniya, sai dai yanayin ciyon da kulawa ne ya bambanta a tsakanin majiyanta da masu lula da su.

Ciyon tavin hankali yana faruwa ne a wasu mabambanta sanadi, wasu sila daga Allah wadda masu ciyon ba su san sababinta ba, wasu kuma yana samunsu ne ta sanadin shan miyagun qwayoyi da basarasa da tabar wiwi da sauran kayan maye, wasu yana faruwa ne a sanadin tsoro da razani da firgita har ma da farinciki. 

Matsalar ta addabi mutane da yawa a wannan lokacin musamman matasa maza da mata da wasu kaɗan daga cikin dattawa a Arewa da Nijeriya gaba ɗaya.

A Sakkwato yanayin asibitin masu kula da tavin hankali yana gamsarwa da tsari, a ziyarar da waƙilinmu ya kai a asibitin kama da bakin ƙofar shiga zuwa wurin gudanar da mulki da wurin duba marar lafiya da dogon ɗakin duba marar lafiya na maza da mata da wurin girka abinci duka za ka gansu da tsafta.

Marar lafiya suna kwance a cikin tsaftar tufafi kaɗan ne za ka gani tufafinsu da datti su ma dai an daganta da barinsu hakan saboda rashin lafiyar su.

A lokacin da waƙilinmu ya shiga makewayinsu ya tarar yana da tsafta, duk da wasunsu ba sa iya zuwa can saboda matsalar rashin lafiyar.

Ma’aikatan lafiya ne ke jinyar mutanen in da suke raba aiki tsari ɗaya da yanda ake kula da masu lafiyar ƙwaƙwalwa a asibitocin yau da kullum.

Abubakar Shagari wani magidanci ne da ya zo karɓar magani ga matarsa da ke fama da ciwon ƙwaƙwalwa waton A’isha ya ce “na fi shekara ina zuwa nan asibitin domin karbar magani ga matata nakan zo duk wata na karɓi maganin ina kashe kuɗi sama da 7000 a wata, maganinsu yana da tsada sosai duk sanda nake zuwa ban taɓa karɓar shi kyauta ba kuma ban ga wani da ake baiwa maganin kyata ba, amma dai maganin nada kyau tsakani da Allah matata na samun sauƙi,” a cewarsa.

Hauwa Muhammed ta ce ita ce ke karɓar maganin da kanta, “ni ne mai ciwon nakai shekara 20 ina shan maganin tun wata matasala dana samu kullum sai na sha maganin nakan karɓi na wata uku duk na zo, maganin yana da tsada sosai, amma yafi cikin gari sauki domin nan asibiti ce can kuma shaguna ne, da za a riƙa ba mu maganin nan kyauta da mun rage wahala da yawa akwai masu son shan magani amma ba su yi don babu halin sayensa sai ka ga ciwonsu na ƙaruwa domin cutar nan ta mu duk wanda bai shan magani ba zai warke ba.”

Mustafa Abu ya zo da marar lafiya ne da ya samu taɓin hankali ya ce yanda tsarin yake a asibitin nan “zan saye katin ganin likita 1000, sai na je a saka bayaninsa, daga nan na je ganin Likita in ya aminta ciwon dole sai ankwantar da shi, za mu biya dubu 63,500, kuɗin duba shi sati biyu, a cikinsu ne kuɗin abincinsa da magani da wanki da wankansa.

“In sun cika ya samu sauƙi shikenan in bai ji ba zai ƙara biyan wasu kuɗin a cigaba da kula da shi har ya samu sauƙi, sai ka biya kuɗin mota a mayar da marar lafiyan gida ko kuma ka zo ka tafi da shi.”

Auwal Isah ya ce yaronsa ne ya kawo ba shi da lafiya an duba shi a watan da ya gabata an ba shi magani, an sanar da shi in ya ga lamarin ba a samu sauƙi ba ya dawo a canja masa magani, shi ne ya dawo yanzu.

“Abin da yafi damuna tsadar maganin na fito daga ƙaramar hukumar Isa na zo nan ga kuma sayen magani da tsada da Gwamnati za ta tausaya ta kawo maganin matsalar ƙwaƙwalwa a kyauta zai taimakawa masu cutar domin abin na wuce wuri in ba a shan magani ga shi da tsada ka saye magani sama da 20,000.”

Nura Tangaza ya ce ɗansa ne ya ke karɓar magani kansa domin cuta ce ta same kan tsaro da ya samu shekara biyar da suka wuce, “duk na zo nakan saye magani na kusan 15,000 sannan na koma gida ban samun tsangwama ta mutanen amma dai maganin ya yi tsada a haka nake ta sayen magani sanda yana kwance kafin a sallame mu da aka yi sallama kuma muka ci gaba.”

Sadiya Keɓɓe ta ce “na kwana ɗaya a wannan asibitin domin sanda na zo ganin likita na saye kati 500 na ganin likita domin ba sabuwa ba ce ni, kafin layi ya kai gare ni sun tashi domin da marece ya yi suke tashi kuma sai gobe, hakan ya sa dole na kwana daga nesa nake, yau likita ya ganni bayan sake biyan wasu 500 wai kullum ake biyan 500 in za ka likita, ya rubuta min magani na biya kuɗi zai kai 20,000 na wata da rabi, gaskiya ya yi tsada maganinsu da ana samun ragi da haka muka so.”

Waƙilinmu ya so jin tabakin shugaban asibitin don sanin shirin da suke da shi a ƙoƙarin rage tsadar magani da tashi likitoci da marece a asibitin a lokacin duba marar lafiya, da bayanin ƙorafin ma’aikata kan walwalarsu, amma lamarin ya ci tura.

Waƙilinmu ya samu jami’in hulɗa da jama’a na asibitin Muhammad Ɗanladi ya ce wanda yakamata ya yi min magana HOD Clinical baya nan, har zuwa haɗa rahoton ba a samu magana da shi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here