Na
Ruƙayya Ibrahim Lawal (Ummu Inteesar)
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
PP 26
ƁANGAREN FATIMA
Fitowa ya yi daga cikin ginin ofisoshin malaman (Faculty of arts/ humanities) ya nufi motarsa yana wani irin sauri mai haɗe da fusata da ta bayyana tsantsa a fuskarsa ya shige motar ya tada ita da ƙarfin tsiya ya zuba speed.
Duk da a cikin makaranta ne ya kuma sani tuƙin ganganci bai dace ba a irin wannan muhallin saboda gudun abin da ka je ya dawo, amma tsananin wutar takaicin da ke ruruwa a zuciyarsa ta makantar da shi daga ganin illar da ke cikin hakan. Alla-alla yake ya gama wannan darasin ya nufi gida don ganewa idanunsa abin da ke faruwa, ba ya jin zai kuma samun cikakkiyar nutsuwa matuƙar bai tabbatar da fitar cikin ba a jikinta. Cikin daƙiƙu goma ya ƙarasa gaban hall 1 in da zai gabatar da darasinsa ya buɗe motar ya kwashe tarkacen kayan aikinsa ya shige ciki fuskar nan ba walwala sam.
A wannan ranar duk yadda ‘yanmatan zamani masu rawar kai suka kai ga hilatarsa da neman samun shiga ta hanyar wurga masa kallon soyayya da kwarkwasa iri dabam-dabam tarkonsu bai yi nasarar kama tsuntsun ba saboda yadda zuciyarsa take a cunkushe.
A maimakon su ga haske ta hanyar karɓar saƙon martanin fara’a daga fuskarsa sai suka samu akasin hakan domin biyu daga cikinsu ma tsawa ya daka musu, da suka miƙe tsaye ya tozarta su a cikin ɗaruruwan ɗalibai ya kora su waje.
Hakan ya sa sauran masu niyyar aikata irin kuskuren suka sha jinin jikinsu suka kame kansu tam ya daina rawar da yake.
A daddafe ya yi mintuna arba’in da biyar daga cikin awa ɗayan da yake da ita ya ba su assignment da doka mai tsauri ta cewar a gobe yake buƙatar takardun amsoshinsu kafin sha biyun rana su tattara su kai masa ofishinsa, kuma submitting individual ne, saboda kowa sai ya yi bayanin tasa takardar amsar dallah-dallah.
Ya tattara nasa inasa ya bar hall ɗin, fiye da rabin fuskokin ɗaliban da ke zaune a cikin suna bayyanar da damuwa mai haɗe da fargaba a kan wannan aikin da ya ba su. Har ma wasu suka fara cece-kuce a kai.
Yana barin nan ya miƙe hanyar main gate da zimmar ficewa daga makarantar sai da ya zo daf da ƙofar kiran waya ya shigo masa. Tsaki ya ja ya ɗauko ta daga gaban motarsa ya duba HOD ɗin department ɗinsu ne yake kira, duk da ba hakan ya so ba amma ya sani ba kira ne da ya kamata ya ƙi ɗagawa ba don haka ya ɗaga.
Bayan gajeruwar gaisuwa a gaggauce ya fara yi masa bayanin dalilin kiran “Ka sanar da sauran staffs namu kowa ya bar abin da yake yi yanzu ku zo nan Faculty ɗinmu mu haɗu akwai tattaunawa mai muhimmanci, abu ne na gaggawa ya ta so.”
“Ok sir.” Ya amsa cikin ladabi da murya mai kauri tare da kashe wayar.
Wani dogon tsakin ya sake ja cike da jin haushin kansa da ya ɗaga kiran, da yanzu ya ficewarsa salun-alun amma ta kama shi dole ya tsaya musamman da ya ji abin gaggawa ne, duk da ma ko ya halarci taron ba ya jin yana da nutsuwar da zai fahimci komai.
Al’amarin Fatima kuwa tun bayan da ta baro gidan su Zinat gidanta ta dawo da ta duba ta tabbatar ta gama gyara ko’ina girki kuma sai azahar za ta ɗaura masa duk da ita ba za ta iya ci ba sai dai ya dawo gidan ya riski ba ta ajiye masa komai ba ma sabon rikici ne mai zaman kansa, musamman a irin wannan lokacin da yake nemanta da rigima ko don samun damar cika mummunan ƙudirinsa na zubar da cikin ta kowanne hali.
Madafar ta je ta duba ta ga da akwai kayan miya da sauran kayan amfanin da za su ishe ta girkin ta ɗebo su ta fara gyarawa ta wanke su tas ta ajiye tana jiran dawowar wutar lantarki da take jira da tsammanin dawowarta wuraren ƙarfe ɗaya na rana.
Ta koma ɗaki ta kwanta cike da tausayin ɗan da ke kwance a cikinta sai shafa cikin take tana surutai ita kaɗai “Allah sarki yarona! Ban san wane laifi ka aikatawa mahaifinka ba yake son ganin bayanka tun kafin zuwanka duniya. Me ya sa a wannan duniyar ba shi da wani babban maƙiyi sama da kai bayan kuma kai ɗin yanki ne na jini da tsokarsa? Ko dai ni ce ba ya ƙaunar haɗa zuri’a da ni?”
Ganin damuwa na son ta yi mata illa kawai ta miƙe ta je ta barkata kayan durowarta ta sauko da su kan gado ta hau sake shirya su wai duk don ta ƙirƙiri abin da zai mantar da ita damuwarta ko don lafiyar ɗan cikinta da ta ji daga baƙin ƙwararrun masana cewa damuwar uwa tana cutar da ɗan ciki.
To duk da wannan ƙoƙarin da Fatima ke ta yi na yaƙi da damuwa makamin nata bai yi kaifin daƙile matsalar da ke addabar ƙwaƙwalwar tata ba sai ma daɗa nutsewa da take yi a cikin kogin tunanin makomar rayuwarta.
Tana cikin wannan halin ne Allah ya kawo mata agajin gaggawa ta hanyar bayinsa da suka maido da wutar lantarki. Ta ajiye tufafin hannunta da hanzari ta nufo falo ta tada kai ta kalli agogon bangon da ke manne sama a jikin bangon da kayan kallo suke. Idonta ya tsaya cak a kan allon agogon da ke nuna ƙarfe ɗaya cif da cif na rana.
Da ‘yar guntuwar murnarta mai nuni da yadda abin ya faranta mata rai ta furta “Ah lallai! Yau ba ƙari ba ragi ko na minti ɗaya. Muna fa shan gata kwanan nan.”
Kai tsaye ta je ta markaɗa kayan miyanta ta zuba su a ƙaramar tukunyar tower ta kunna electric ta ɗora a kai domin su tsane ruwan jikinsu.
Ta fito daga madafar kenan ta jiyo sallama a ƙofa, ta shaida muryar Sajidah tun kafin fuskarta ta bayyana a gaban ta. Da murnarta ta tafi da ɗan gudu ta rungume Sajidan tana yi mata maraba da zuwa.
“Kai anti Fati wai ke har yanzu ba ki girma kin daina wannan abun ba?”
Hararar wasa ta aika mata. “Dube ta don Allah! Da can ni wata babba ce? Sa’anni ne fa ni da ke don kawai na taimaka na auri wannan dattijon yayan naki ne kike wani tula mini girma.”
“Kai anti Fati! Ban da sharri kuma, du-du-du yayan fa bai kai 34 ba kike kira masa tsufa.”
“Ni kuma ai ban fi 22 ba har yanzu kin ga kuwa tsoho ne a kaina.”
Cike da raha ta ja hannunta suka ƙarasa ɗakin suka zauna a falo ta kunna musu kayan kallo suka fara kallon tashar Zeeword sannan ta miƙe ta je ta ɗauko mata ragowar maltinar da ta bari jiya a fridge da ruwan roba ta ajiye mata.
“Sajijin hajiya ga wannan ki fara taɓawa kafin na ɗaura girki kin san fa yayan naki sai yamma yake dawowa shi ya sa ba na ɗora girki da wuri.”
Ta yi zancen tana yunƙurin zama bayan ta gama daidaita zamanta ta ci gaba da cewa, “Kafin nan ma ko indomie ce sai na girka miki…”
Saurin yi wa bakinta linzami ta yi da ta tuna cewa ashe fa jiya da muguntar tasa ta motsa ya kulle duka wani abincin gidan, sai da safe ne da zai yi musu girki ya fito da buhun shinkafa kawai shi ma ta lura da hakan ne lokacin da ta je gyara kitchen ɗin da ya ɓata.
Jin ta yi shiru ga kuma yanayin fuskarta da ya fallasa asirin zuciyarta ya saka cikin fara’a Sajidah ta ce “Kar ki da mu anti Fati ai ni ba baƙuwa ba ce, ba ma jimawa zan yi ba, hajiyarmu ce ta turo ni na duba mata lafiyarki don ta damu da jin ki shiru tsawon wata biyu ba ki leƙo mu ba.”
Murmushin yaƙe ta yi a ƙoƙarinta na ɓoye gaskiya ta ce “Uhm! Lafiyarmu qalau wallahi, sabgogin rayuwar ne da yawa…”
Ta miƙe a yunƙurinta na noƙewa zancen, ta nuna hanyar waje da yatsa tana cewa “Bari na duba kayan miyan.”
Da hanzari ta nufi wajen tana hura iska da baki tare da wulƙita idanuwa, ba fatanta ba ne ta rufa masa asiri sai dai ba ta son jefa mutanen da suke ƙaunarta a cikin damuwa. Ta sani surukar tata tana matuƙar son ta ga sun ajiye mata jikoki domin lokuta da dama tana gano tsananin ƙaunar surukar tata ga jikoki ta cikin kalaman da take furta mata duk da tana nuna mata kawaici irin na sarakanai sosai.
Sanin halin da ɗanta yake ciki na nuna tsananin ƙiyayya ga abin da ta fi ƙauna kan iya jefa ta cikin matsananciyar damuwa ita ko ba za ta so hakan ba shi ya sa take jurewa.
Tana shiga kitchen ɗin tun kafin ma ta yi abin da ya kai ta ta jiyo motsi a bayanta, juyowar da za ta yi haka ta ga Sajidah tsaye a bayanta hannunta riƙe da gwangwanin maltinar da ta ba ta.
“Anty Fati bari na taya ki.” Ta girgiza kai alamar a’a.
“Da kin bar shi Sajiji ai aikin ba yawa.”
“Ni dai sai na taya ki sai dai kuma idan kora ta za ki yi.” Ta yi furucin tana matsowa kusa da ita.
“Wace ni na kori maigidan da kansa?” Fatima ta furta tana dariya.
Haka suka fara aikin a tare gwanin ban sha’awa, bayan ta buɗe warin tafasar shinkafar ya daki hancinta nan da nan ta ji kayan cikinta sun hautsine, ta fara jin tashin zuciya amma da ke ba ta son Sajidah ta ɗago komai sai ta dake ta ɗauko gwagwa da ƙaramin bokiti ta ɗaura gwagwar a kai, ta fara ɗebo shinkafar tana zubawa a kai kenan abin ya taho gadan-gadan, ta yi wani dogon yunƙuri ta saki robar da ke hannunta ta fita da gudu sai dai tun a ƙofar kitchen ɗin daga waje ta ci burki ta durƙushe a gun ta fara zubo aman ba ƙaƙƙautawa. Cike da ruɗewa Sajidah ta yo gunta tana dafa kafaɗunta ta baya “Subhanallahi! Anti Fati dama ba ki da lafiya ne?”
Shiru ba amsa ta fara jera mata sannu sannan ta je ta ɗebo ruwa a buta ta kawo mata. Sai da ta amayar da komai da ke cikinta sannan ta samu nutsuwa ta wanke bakinta da fuskarta, Sajidah na faman jera mata sannu ta miƙe tana dafe saitin zuciyarta tare da gyaɗa mata kai sama alamun amsawa.
Ɗan ƙauri-ƙauri hancin sajiidah ya jiyo mata sai a lokacin ma ta tuna aikin da suke a kitchen ta faɗa ciki da sauri tana faɗar “Innalillahi! Girkinmu.”
Ba ta yi wata-wata ba ta ɗebi ruwan da ke ajiye a wani ɗan bokiti wanda Fatiman ta shigo da shi musamman don yin aikin ta zuba cikin shinkafar ta ɗauko matsamin ƙarfe da ta gani sarƙafe a jikin saitinsa a bango ta tono ƙasan. Shinkafar ce ta fara kamewa kaɗan saboda ƙarfin wutar da ke akwai ga electric ɗin ba mai control ba ne kai tsaye ne.
Sai dai an yi sa’a ba ta kone ba don haka ta ƙarasa aikin da Fatin ta fara ta mayar da shinkafar a tukunya ta zuba ruwa kaɗan ta rufe ta juya miyar ta fice.
A cikin baranda ta samu Fatiman zaune a kan tabarma tana mayar da numfashi, alamomin gajiya duk sun bayyana a fuskarta.
“Sannu anti Fati, da ma wai ba ki da lafiya ne?” Ta furta tana yunƙurin tsugunnawa kusa da ita.
Ta girgiza kai alamun a’a. Sajidah ta yi kyakkyawan murmushi da ya ƙarawa fuskarta mai kama da ta yayanta Musa kyau cikin sigar zolaya ta ce “To ko mun samu ƙaruwa ne?”
Gaban Fatima ya ba da ras jin wannan tambayar, tana son ba da amsa ko don samarwa rayuwar abin cikinta ‘yanci, amma zahirin gaskiya tana tsoron abin da zai je ya dawo don ta san Musa ba zai so hakan ba, amma fa wannan kyakkyawar dama ce a gare ta.
Wannan karon ta murje ido ta ƙi yin biyayya ga zuciyarta ta yi abin da take ganin shi ne daidai ta hanyar ɗagawa Sajidah kai alamar eh tare da saka tafukan hannayenta ta rufe fuskarta alamun ta ji kunya.
Farin ciki ƙarara ya bayyana a kan fuskar Sajidah har da ihun murnarta ta miƙe tana faɗar “Allah ya nina ya raba lafiya, kin ga yanzun nan zan koma gida na yi wa hajiyarmu albishir, wannan goron ba zan bari ya zama rabon wani ba.”
Ta faɗa ɗaki tana tattaro mayafinta da jakarta ta fito haƙora a washe.
Ba yadda Fatima ba ta yi da ita a kan ta tsaya girkin ya kammala ta ci ba fur ta ƙi. Sai da ta zo wucewa za ta fita idanunta ya sauka kan ƙazantar da matar yayan nata ta yi da har murna ta mantar da ita.
Ba ƙyanƙyanin komai ta je ta ɗauko tsintsiya da ruwa ta gyara gun tsaf ta wanke tsintsiyar ta maida ta muhallinta sannan ta ƙara yi wa Fatima sallama ta fice.
Ficewar Sajidah kedawuya ta ji kamar an ƙara mata kuzari ta miƙe ranta wasai ta je ta ƙarasa girkinta ta sauke ta rufe a kuloli.
Sai lokacin ta samu nutsuwa ta koma falo kenan sai ga wasu biyu daga cikin ‘yanmatan layin sun zo kallo, ba ta hana su ba suka baje a falonta ana yi.
Ba wani fahimtar abin da ake yi take a tvn ba maimakon a ce ita take kallon shi to shi ne yake kallonta. Ita dai ga ta nan ne saboda zaɓar yunwa da take ji kamar ta ci babu, ga ta da lafiyayyen girki ajiye sai dai ba ta isa ta gwada ko ɗanɗanawa ba idan tana son kanta da lafiya.
Taliyar manja da mangwaro take kwaɗayi kamar ta sato sai dai ba kuɗi a hannunta ga shi roƙo ba ɗabi’arta ba ce ballantana ta aika maƙwafta ko za ta samo. Kuɗin da Innanta za ta turo mata kuma shiru ba labari har lokacin.
Tana cikin waɗannan tunanukan bacci ya fige ta sama-sama. A ɗan baccin na mintuna har da mafarkin ta ci taliya daga ƙarshe ta gan ta ɗare-ɗare a bishiyar nunannen mangwaro tana tsinka tana sha.
Sallamarsa ce ta karaɗe falon, ‘yanmatan suka amsa suna gaishe shi ya shiga ciki. Tsayuwa ya yi ta ‘yan sakanni a kanta yana so ya gano yanayinta, sai ya fuskanci kamar baccin nutsuwa take, take ɓacin ran da ya taho da ɓurɓushinsa ya sake ninkuwa ya bubbuga kafaɗarta da ƙarfi “Ke ta shi don Allah!”
Firgigit ta buɗe idonta tana faɗar “yanzu zan sauko jira na tsinko na ƙarshe….”
Ƙarashen zancen ya maƙale a ƙasan maƙoshinta lokacin da ta gama buɗe idonta ya sauka a kan kyakkyawar fuskarsa da take a haɗe tam.
Ajiyar zuciya ta sauke tana furta “Wai har ka dawo ne?”
Sautin ‘yan wasan dramar India da ake haskawa da turanci ya daki kunnenta abin da ya tuna mata da yanayin da suke ciki kafin baccin ya sure ta. Nan da nan ta haɗe fuska ta hau rarraba idanu a cikin ɗakin tana neman ‘yanmatan da suke kallon tare sai dai abin da ba ta sani ba tun da suka ga shigowar maigidan suka miƙe suka bar gidan gabaɗaya don sun san abin da ka iya faruwa idan ta farka ta gan su ga kuma mijinta. Ba za su iya da sabgar kishinta ba ne ya sanya sawunsu a likkafa suka yi gaba.
Duban tsaf ya yi mata a lokacin da take dube-duben ya mayar da fuskarsa a yanayin ba yabo ba fallasa ya ce da ita “Ya jikin? Ba dai abin da ya same ki bayan na fice ko?”
Ta dawo da dubanta a kansa tana girgiza masa kai da faɗar “Ba komai alhamdulillah! Sai ƙarfi ma da na ƙara samu.”
Bai ƙara tamka mata ba tsabar baƙinciki da ya haɗu ya masa yawa ya wuce zuwa ɗakinsa yana mita a ransa ‘shashashar mata sai masifar kishi amma ba ta ma san ya ake kula da miji ba.’
Bayan baƙincikinsa na tarar da abin da ya tsana sai kuma ga shi ta ƙara ƙular da shi, wai a ce ya shigo rai a ɓace amma ita sam ba ma ta lura da hakan ba ballantana ta tambaye shi dalilin ɓacin ran nasa ko ta yi ƙoƙarin tarairayarsa da lallashinsa ya rasa me ke yawo a cikin kanta, ita kawai irin mutanen nan ce ‘yan i don’t care, duk abin da ba su ya shafa ba ba su wani damu da shi ba.
Miƙewa ta yi ta je ta shigo masa da abincinsa ta ajiye a nan falo, ba ta yi yunƙurin bin shi zuwa ciki ba saboda ta san galibi da ya dawo yake shigewa sai ya yi wanka zai fito ya ci abinci ya fita.
Shigowa yana shigewa ya mayar da ƙofarsa ya rufe ta ciki ya fara laluben number yayarsa Dije Danger tana shiga cikin sa’a ya ɗaga kamar mai jiran kiransa tun can da.
Da muryar damuwa ya fara magana “Yaya akwai matsala fa, kin gan ta can tana sabgoginta ko alamar sauyi babu a tare da ita, sai ma ƙarfin jiki da ta ce ta ƙara samu.”
Daga can ɓangaren yayar ta amsa da “Kuma duka ƙwayoyin biyu ka tabbatar ta sha su?”
“A’a guda ɗaya na bada dake da dabara ne ba na so ta zargi komai, kin san dai na labarta miki abin da ya faru a wancan cikin.”
“Ai ka ji irinta mai sunan malam kai ka ɓata komai, a tare suke aiki ai. Kawai ka sake haɗa biyun ka ƙara mata idan ka ga an kwana a haka ba sauyi. Zuwa gobe ko jibi idan ba ta sauya zani ba da kaina zan zo gidan sai mu ɓullo mata ta bayan gida.”
Da wannan suka kawo karshen tattaunawarsu ya ɗan ɗosana mazaunansa kan dressing mirrow yana dafe goshi da sauke huci.
UMMU INTISAR CE