Home Daga Marubutanmu RAUNIN RAYUWA: Fita Ta 25

RAUNIN RAYUWA: Fita Ta 25

9
0

PP 25

ƁANGAREN HALISA

Waiwaye Adon tafiya.

Malam Saminu Gorau ɗan asalin jahar Sokoto ne tun lokacin manyan jahohi uku suna a haɗe kafin a rarraba su har a sake cire wasu jahohi biyu a cikin sokoton wato Kebbi da Zamfara.

Shi haifaffen garin Sifawa da take ƙarƙashin ƙaramar hukumar Bodinga ne don akwai wannan garin tun zamanin Shehu Usman Bin Fodio.

A shekarar 1980 bayan an ba wa jahar Sokoto matsayin state a hukumance ya baro ƙauyensu ya dawo zama a cikin birnin domin kasuwanci lokacin yana da shekaru 45 a rayuwarsa.

Ko da ya yo balaguron yana da aure matansa uku Habiba, Halisatu(Ige) da Barira sai yaransa guda goma.

Habiba tana da biyar Garzali, Shatu, Labiba, Hafsatu da Tanko. Halisatu tana da uku Mariya, Bello da autansu Halilu.

Yayin da Barira take da yara biyu kacal Tukur da Salmanu.

Farkon zamansa a Sokoto yana zaune ne a wani madaidaicin gida a wajen gari ta gefen ƙofar taramniya saboda tun lokacin da ya sauka garin gidan maigari ya yi wa tsinke sai da ya kwashi gaisuwa a gun mai martaban sannan ya gabatar da kansa a matsayin baƙo da dalilin da ke tafe da shi.

Jin cewa yana da iyali ya saka maigarin ya tashi biyu daga cikin dogaransa ya saka suka raka malam Saminu zuwa filayen bayan gari inda aka ware musamman don saukar da baƙi ire-iren shi ya nuna daidai filin da yake jin zai ishe shi aka kewaye masa shi bisa ga umurnin mai gari ya fara gini.

Sai dai kafin ya kammala ginin an sauke shi a wani ƙaramin gidan saukar da baƙi da maigarin yake da shi a nan cikin ƙofar Taramniya.

Haka ya fara sana’arsa a can inda yake ginin, don ya lura ma fiya yawan mazauna wannan wurin baƙi ne masu sana’ar rini, daɗin zama ya saka suka kafa ‘yar kasuwa a gun ana kiran wannan unguwar Marna.

A wannan kasuwar ya fara sana’ar fawa da ya gada daga mahaifinsa. Yakan je babbar mahautar garin ya sayo rago a gyara masa shi ya sako naman a baro ya turo har cikin kasuwar ya kasa a teburinsa.

Allah ya tarfawa garinsa nono yana da nasibi sosai a cikin sana’ar wani zubin don rago uku duk sai ya yanka ya sayar da su a cikin abin da bai fi wuni biyu ba.

Kan ka ce kwabo har jarinsa ya ruɓanya ya fara sayan dabbobi yana sayarwa ƙananun ‘yan kasuwa na ƙasan shi yana haɗa ribarsa.

A daidai wannan kaɗamin ne ya tare a babban gidansa da ya gina a Marna suka ci gaba da rayuwa a ciki shi da iyalansa. A shekarar 1982 ya halacci sallar idi ta farko a wani babban masallacin idi wanda aka yanki jeji mai matuƙar girma aka ƙaddamar da shi a matsayin masallacin idi kaɗai.
Dubbannin musulmi mazauna jahar sun yi sallah cikin farinciki da kwanciyar hankali aka watse, a wannan zuwan ne ya gano wasu gidaje jefi-jefi a gefe.

Gidajen ba su fi biyar ba a nan ya tabbatar da ba a jima da fara yankar filayen zama a gun ba. Wurin ya matuƙar burge shi musamman saboda kasancewarsa nesa da cikin gari sosai ga ire-iren shi mutanen da ba su cika son hayaniya ba wuri ne da zai yi musu daɗin zama sosai. Tun a lokacin ya ƙwallafa rai da mallakar fili a gun Amma ya yanke sai ya ƙara ganin kan garin kafin nan ma ya san wurin ya ɗan ƙara cika da jama’a sai kawai ya mayar da iyalinsa can.

Bayan shekaru uku kuwa ya je gidan sarki bayan ya yi nasarar ganawa da shi da jiɓin goshi, ya gabatar da buƙatarsa cikin sa’a ya samu karɓuwa aka ba shi izini ya je ya yanki babban fili a hoƙon idin da ya fi na Marna girma ya tada ginin babban gida har da yaɓe.

Yaransa sun taso cikin walwala, ƙaunar juna da haɗin kai. Sai dai matan ne akwai ‘yar tsama a tsakaninsu musamman Halisatu da Barira da ba su cika shan Inuwa ɗaya ba saboda Halisatu rigimammiyar mace ce mai matuƙar son yaranta duk wanda zai taɓa mata su kuwa ba sauran shiri a tsakaninta da shi.

Ita kuma Barira akwai neman magana da ganin ƙyashi sai dai duk wannan abin da suke bai shafi zumuncin yaransu ba Allah ya katange musu zuciya daga hassada suna ɗaukar junansu a matsayin ɗaya.

A shekarar 1985 Allah ya amshi rayuwar Alhaji Saminu, iyalansa sun shiga damuwa matuƙa da wannan babban rashi da suka yi na jigon rayuwarsu, musamman yaransa da sai a wannan shekarar babban ɗansa Garzali ya cika shekara ashirin da uku a duniya.

Sai dai ba a rufa kyakkyawan wata ɗaya ba Barira ta tada rigima a kan a raba gado a ba ta haƙƙin yaranta. Ba a ɓata lokaci Garzali ya je ya nemi manyan malamai suka shiga lamarin, aka yi kasafin dukiya da kadarorin mahaifin nasu kowa ya aka fitar masa da nasa kamar yadda shari’a ta tanada, shi ne Ige ta tsira da ƙofa ɗaya haƙƙin ‘yarta Mariya, daga baya bayan ƙarfin yaranta ya kawo suka tada katanga suka killace mata ƙofar tata aka saka ƙyaure, sai ya zamana ita ce a farkon shigowa gidan, sauran matan da sarakanansu kuwa suna can ciki a haɗe wuri ɗaya.

Ba a rufa shekara ɗaya da mutuwar Alhaji Saminu ba duka matan nasa biyu suka rasu iya Ige ce kadai ta rage. Dalilin da ya saka ta zama jagora a gidan kenan don ita kaɗai ce a mazaunin uwa gare su.

Yaran suna girmamata da ba ta matsayinta hakan nan ba su lamuncewa matansu ko ‘ya’yansu su raina ta ba, sai dai su yi a bayan idanunsu. Su ko su Shatu, Labiba da Hafsatu da Mariya tuni suka yi aure suka fara tara tasu zuri’ar.

A wancan zamanin na baya Halilu babban bakanike ne tun lokacin samartakarsa shi ya ja ƙaninsa Tukur wanda tsakaninsu shekara ɗaya ne da wata shida ya kai shi kasuwa ya koya masa sana’a da ya tabbatar ya iya kuma ya ba shi jari.

Duk wata kulawarsa ya ɗauka ya ɗora ta a kan Tukur kasancewar shi ba shi da ƙani a ɗakinsu yana matuƙar ririta shi har zuwa lokacin da ya fara haihuwa duk Halilun ke sayawa yaransa ragon suna ashe bai san ta ciki na ciki ba.

A fuska nuna yake ba shi da wani masoyi sama da yayansa sai dai wannan iya abin da yake nunawa jama’a ne a zahiri amma a can ƙasan ransa yana matuƙar hassada da yayan nasa kasancewar ya fi shi nasibi a duk harkokin rayuwarsu, a gefe ɗaya kuma mahaifiyarsa Barira ta taka rawar gani wurin hura wutar ƙiyayyar yaran Halisatu a zuciyar yayanta tun suna ƙananu. Dalili kenan da ya saka duk abin da Halilu ko ‘yan’uwansa za su yi ba sa gani.

Dawowa daga labari

Al’amarin Halisa kuwa sai abin da ya ci gaba, a maimakon tana daɗa girma hankali yana shigarta sai ya zamana rashin jin nata ne ke daɗa girma a tare da ita, tsokana sai abin da ta manta ko wanda bai zo mata a kai ba.

Watarana suna kan hanyarsu ta dawowa daga zana jarabawar su ta kusa da ƙarshe ta WAEC da suke yi, sai da aka gama sauke kowa ya rage saura ita kaɗai ya gangaro da ita cikin unguwar tasu kenan napep ɗin ta tsaya cak.

Dogon tsaki ya ja yana girgiza sitiyarin da faɗar “Da alama fa mai ne ya ƙare.”

“O’oe! Kuma don tsiya man bai tashi ƙarewa ba sai da ya rage saura ni kaɗai?” Ta wurgo magana daga seat ɗin ba ya da take zaune alamar ranta ya sosu.
Bai amsa mata ba don a ganinsa wannan ba tambaya ce da take buƙatar amsa ba don haka ya mayar da hankali gun neman mafita.

Ya fita ya zaga ta inda bututun man yake ya buɗe ya leƙa ya girgiza napep ɗin, duk wata dabara da ya san za ta fitar da shi sai da ya jarraba ba ta yi aiki ba. Ya duba gefe da gefensa ko zai hango ‘yan black market amma da alama babu su a kusa da gun.

Zura kansa ya yi cikin boot ya ɗauko garloon ya fitar da kansa waje yana kallonta. “Ƙanwata sai ki yi haƙuri ki fita daga nan ki ƙarasa a ƙafa, ai saura kaɗan ma mu ƙarasa inda kika kwatanta mini. Yanzu ni dole zan je nemo fetur.”

Fuskarta ba yabo ba fallasa ta fito tana faɗar “Gaskiya ba ka kyauta mini ba kasan kuwa irin gajiyar da na yi?”

“Haƙuri za ki yi, ai duk ba haka muka so ba.”
Juyawa ta yi ta kama hanya ya ɗan ɗaga murya kaɗan “Kuɗin nawa fa?”

Ta juyo tana sako masa manyan idanunta da murya mai nuna tsantsar mamaki ta ce “Innalillahi! Yanzu kana nufin duk wannan wahalar da ka saka ni ni ma sai na biya?”

Shiru ya mata kawai yana kallon ta ta fara laluben aljihun wandonta tana faɗar “Shi kenan bari mu raba hasara.”

Naira arba’in ta ciro ta miƙa masa tana faɗar dama saba’in-saba’in kowa ta biya, ni kuma zan bada haka tun da ai ba ka kai ni duka ba.”

Mai adaidaitar ya zo iya wuya don haushi kuma ya lura da gaske take don haka ya riƙe hijabinta yana faɗar “Idan ma kin saba yi wa wasu irin wannan iskancin ni ba zan ɗauka ba, ba inda za ki tafi sai kin cikan kuɗina.”

Kallon rainin hankali ta bi shi da shi tana faɗar “Idan kana son cikon kuɗin ka cika mini tafiyata.”

Ta buga aljihun wandonta tana ci gaba da faɗar “Ka gan su nan wallahi ina da su na cika maka ne ba ni da. Hijabin kuwa bari ka ga…”

Ta saka hannu ɗaya ta yaye hijabin ta bar masa shi a hannu kenan Allah ya jefo wani bawan Allah da tun daga ɗan nesa yake hango abin da ke faruwa ya zo da gudu ya cire hijabin daga hannun ɗan sahu da ya sake baki da hanci yana kallon ta ya ma kasa sake hijabin haka nan kalma ɗaya ta ka sa samun ‘yancin kuɓutowa daga bakinsa zuwa waje.

Miƙa mata hijabin mutumin ya yi tare da tambayar ba’asi.

Mai napep bai rage komai ba daga abin da ya faru ya sanar masa. Hannu mutumin ya saka a aljihun gaban rigarsa ya ciro ɗari biyu ya miƙa masa yana faɗar “Yi haƙuri ɗan samari karɓi wannan ka tafi.”

Ya juya gare ta yana ci gaba da faɗar “Ke ma ‘yanmata je ki abinki Allah ya shirye ki.”

“Amin Amin.” Ta amsa da gadara sannan ta juya ta tafi bayan ta mayar da hijabin nata tana magana ƙasa-ƙasa “Da ji yake ya fi ni tijara, ni da ke mu’amala da su Timaya har a gaya mini tashanci? Ai wallahi tun kan ai ɗaram a kai Kwanɗi. Na so mutumin nan bai zo ba in ga uwar abin da wannan ƙurungun zai iya.” Ta kama hanyarta tana tafiya.
Wani layi ta bi da nufin yin ratse, ta ɗan yi nisa kaɗan idanunta suka sauka kan wani sirɗeɗen matashi tsaye a ƙofar wani gida, nan da nan ta nemi guntun ɓacin ran ta rasa ba ma ta san lokacin da ta bushe da dariya ba tana yi tana matsawa kusa da shi. “Tabɗijam! Ka ga wani tsololo? Tsamarƙe suna ga wani.”

Hankalin dogon matashin ya dawo kanta sai kallonta yake amma ita ko a jikinta sai ma ƙarasawa ta yi daf da shi ta tsaya ta ce da shi “In faɗa maka wani abu bawan Allah?”

Samun kansa ya yi da gyaɗa mata kai alamar eh.

Cikin sautin dariya ta fara magana “Gaskiya ubangiji ya yi halitta a nan, kai kyakkyawan gaske ne tsawon ne kawai ya maka cikas, da za a iya rage maka shi komai normal.”

Ta buɗe tafin hannunta ta lanƙwasa yatsa guda biyu manuni da babban sauran ukun suna a miƙe ta girgiza su alamun komai ya yi.

Bai san ya aka fara ba ya tsinci kansa da yin murmushin da ya bayyana haƙoransa ya ce da ita “To na gode ‘yanmata.”

Ba ta ƙara yi masa magana ba ta ci gaba da tafiya tana tsalle-tsalle da tafe-tafe. Murmushin kan fuskarsa ya kasa gushewa ya bi bayanta da kare-kare har ta ƙarasa gidansu ta shige.

A ransa ya ce ‘Da alama zuciyarta tsarkakakkiya ce kawai wasa ce ta mata yawa.’

Ƙarar ringin wayarsa ne ya farauto shi daga duniyar batun zuci. Ya saka hannu a aljihun wandonsa ya ciro ta ya ɗaga tare da ɗorawa a kunne.

Daga can ɓangaren muryar namiji ta bayyana yana faɗar “Kai ina ka je ne? Na ɗauko takardun na fito kuma ban gan ka a ƙofar gida ba.”

“Afwan na ɗan matsa gaba ne, wani abu ne ya ja hankalina gani nan dawowa yanzu. Ka jira ni a wajen yanzu za ka gan ni ba fa nisa na yi ba.”

Daga can ɓangaren aka yanke kiran, ya juya ya matsa zuwa gun kantin da ya gani kusa da ƙofar gidan ya yi sallama. Bayan sun gaisa da mai kantin ya siffanta masa yarinyar tare da tambayar shi sunanta, kuma yana so ya tabbatar ko a gidan da ta shigan take.

“Oh! Apsara kake nufi, ita ce dai ta wuce yanzu. Yarinya ‘yar gaban goshin kakarta, nan ne gidansu. Kai ma ta yi maka halin nata ne za ka kai ƙara?” Mai kantin ya tambaya.

Girgiza kai ya yi alamar a’a sannan ya yi wa masa godiya ya juya ya koma gidansu Kasim (course mate ɗinsa a jami’a) .

Da ma ya shigo unguwar ne don karɓar takardun assignment ɗinsu wanda a gobe ne suke tsammanin malamin nasu zai karɓa, team work ne ya kuma lura cewar idan ba shi ɗin ba ne ya yi ba wanda zai mayar da hankali a yi. Takardun kuma suna hannun Kasim shi ne ya takura a kan zai zo gida ya same shi su zauna su fitar da abin da za su iya sai su je shagon printing a buga musu. Yana cikin tsayuwar jiran fitowar Kasim ɗin ne kuma kwatsam Allah ya jefo wannan budurwar da ya ji ta shiga ransa farat ɗaya.

Duk da cewa tsokanarsa ta yi to amma shi sam bai ji haushi ba sai ma burge shi da ta yi. A rayuwarsa yana don ganin mutum ya kasance straight forward (mai faɗar abu kai tsaye) ya kuma lura kamar tana ɗaya daga cikin rukunin mutanen tun da ta kasa jurewa sai da ta tamka a kan tsawon shi.

Bai san abin da Ubangiji ya tsara game da haɗuwar tasu ba sai dai ya ji a zuciyarsa ba haɗuwar banza ba ce dole akwai dalilin da ya saka hakan ta faru. Shi ne kawai ya yanke shawarar bin bayanta a zuciyarsa ya kuma aikata hakan domin ba a san me gobe za ta haifar ba.

A yi haƙuri da wannan in sha Allahu idan na warware komai zai dawo normal

Ummu Intisar ce

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here