Na
Ruƙayya Ibrahim Lawal (Ummu Intisar)
MARUBUCIYAR;
SOYAYYAR MEERAH
YAR GANTALI
RIKICIN MASOYA
A SANADIN KAMA
HALITTAR ALLAH CE
WATA UNGUWA
GIDAN DUHU
SHARRI KARE NE…
WATA DUNIYA
ƊANYAR GUBA
AND NOW
RAUNIN RAYUWA
AREWA WRITERS ASSOCIATION
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM
PP 24
ƁANGAREN SURAYYAH
Ƙara saurin tafiyarta ta yi ta isa inda Surayyar ke zaune ta dafa bayanta.
Da ƙarfi ta zabura ta ɗago kanta a firgice don ganin wa ya taɓa tan.
A nan ganin maman ya sauka a kan idanun Surayyar da suka yi luhu-luhu fatar ƙasan idon ta yi ja sosai kamar ɗanyen nama. Da ɗan firgici ta ja da baya tana furta “Subhanallahi! Ke me ya same ki haka? Kin ga fuskarki kuwa?”
Ta tambaya tana ƙara kallon fuskar Surayyah da ta kumbura sosai alamun ta sha kuka mara iyaka.
Cikin sautin kuka ta fara magana da muryarta da ta dusashe. “Mama Ahmad ne fa…” Sai kuma kukan ya sake ƙwace mata ta sake sakin shi da ƙarfi.
Wannan yanayin da ta shiga ya ƙara dugunzumar da hankalin mama, ‘Kar dai a ce mutuwa ya yi.’ zancen da ya kawo ziyara a harabar filin zuciyarta kenan da ya ƙara hauhawar da farashin tashin hankalinta ta fara magana a dabarbarce “Me ya samu Ahmad ɗin? Hatsari ya yi?”
Ta girgiza kai alamar a’a. Maman ta sake jefa mata tambaya “Ba shi da lafiya ne?”
Nan ma alamar a’a ta yi mata hakan ya saka maman ta nemi wuri a kusa da kujerar da take kai ta zauna tana faɗar “To ki kwantar da hankalinki ki faɗa mini me ya same shi. In Sha Allahu za mu nemo mafita komai zai zo da sauƙi.”
Ta ƙarashe zancen da sigar lallashi.
Dogon numfashi ta ja ta sauke kafin iya cewa.
“Ahmad ya ce ya fasa aurena mama.” Ta yi furucin tana sakin marayan kuka, kamar wacce aka saukowa da wahayin mummunan labari mama ta zabura ta miƙe da ƙarfi tana maimaita faɗar “Innalillahi wa inna ilahir raji’un!”
‘Yan sakanni ta kwashe a haka kafin yanayin kan fuskarta ya canza zuwa na tuhuma ta saukewa Surayyah gajiyayyun idanunta tana faɗar “Ki faɗa mini gaskiya, me kika yi masa? Na san dai haka siddan ba zai fara wannan aikin ba.”
Cikin muryarta mai fallasa tsantsar gaskiyar da ke ƙunshe a zuciyarta ta ce
“Wallahi mama ni ma abin da na kasa ganewa kenan. Juyin duniyar nan na yi ya ƙi bani amsa gamsasshiya sai wannan saƙon da ya turo mini.”
Ta ɗauko wayarta da ke kan hannun kujerar tana zana zanen sirri(pattern) na buɗe wayar, ta shiga saƙon ta miƙa wa maman.
Galala ta buɗe baki tana kallon ta “To karatu kika san na iya ne ko kin yi da nufin tozarta ni ne? Miƙa wa A’ishatu ta karanta mini.”
Ba ta iya yin magana ba sai cika umurnin maman da ta yi, ba ɓata lokaci A’ishatu ta karanto saƙon nasa a fili yadda kowa zai ji.
Sallallami mama ta shiga yi ta koma ta zauna cike da Jimami sai dai har yanzu ta kasa yarda cewa Ahmad ba shi da wani dalili na rabuwa da ‘yarta.
Murya a sanyaye ta sake cewa “Kin ga Surayyah idan kin san laifin da kika yi masa ki faɗa mini mu san ta inda za mu ɓullowa lamarin kafin zancen nan ya baza unguwa.”
“To ni dai a iya sanina ba ni da wani laifi, idan ma laifi ne shi ne mai shi tun da…” Sai kuma ta yi shiru da ta lura cewa tana shirin yin katoɓara. Maman ta kaɗa ta raya Surayyan ta ƙara zancenta amma fur ta ƙi, ganin haka ya sa ta kuɗurce wata shawara a ranta ta bar ta a cikinta.
Yanayin da ta shiga bayan jin kalaman ‘yar tata ya saka kuɗirin watsa ruwa da ta shigo da shi ya bi shanun sarki nan ta kishingiɗa kan doguwar kujera bayan ta rage tufafin jikinta, ta yi shiru idanunta na kallon gefe alamun ta shiga yanayin damuwa da dogon tunani.
A’ishatu ba ta yi magana ba sai taɓe baki da ta yi ta ɗebi yayar ta watsar ta miƙa mata wayarta kawai ta nufi madafa don ganin me Surayyar ta girka musu.
Ɗakin ta nufo tana masifa da yaɗa ƙananun maganganu. “Haba anty Surayyah tuwon dawa fa? Sai ka ce a ƙauye? Ke kin san dai ba na son shi shi ya sa kika girka shi da gangan.”
A cikin yanayin da Surayyah take sam ba za ta iya wata masifa ba don haka ba ta kula Ayashern ba don yasan komai da take yi don maman ta riƙe mata kan ɗan majici ne ya sa take wasa da jelarsa, ta miƙe jiki ba ƙwari ta fita waje don watsa ruwa ta fara shirin tafiya gidan kakannin nasu don yau da wuri take so ta shige ko don yadda ta ji kanta ya matsa mata da sarawa.
Tana sako ƙafarta waje iska mai ƙarfi ta fara kaɗawa tana buga gyauren ƙofar gidan kamar haɗin baki nepa suka kashe wutarsu. Ta ɗaga kanta sama ta ga yadda hadari ya lulluɓe sararin samaniyar sai walƙiya ke wulgawa wulwul.
Da hanzari ta koma ciki ta ɗauko Torchlight ta je banɗaki ta watsa ruwan a gaggauce, riga mai sassaucin nauyi ta saka sannan ta zumbula hijabinta ta yi sallama da mama ta fice cikin sauri kamar za ta wuce ƙafarta, ba ta son ruwa ya tare ta a hanya ga shi a ƙasa za ta tafi.
Tafe take tana addu’o’in fatan kada ruwan ya sauka sai ta isa, sai dai ta fi rabin tafiyar da kaɗan ruwan ya tsuge da ƙarfi don ko yayyafi ba a yi ba da ƙarfinsu suka taho.
Ba yadda ta iya dole hakan ta ci gaba da ratsawa cikin ruwan tana ƙanƙame jikinta ta ɓulla ta kan titi ta ci gaba da tafiya. A da ta fi yin ratse ta bi ta layuka har ta je gidan amma ruwan na sauka a yau sai ta zaɓi ta fito kan kwalta ta ci gaba da tafiya saboda gudun hatsarin da ka iya samuwa a layukan; Za ta iya jefa ƙafarta a rami ko ta yi karo da wani tsautsayi a gun da ba yawaitar motsin mutane, shi ya sa ta yi wannan zaɓin da take ganin shi ne kyakkyawa.
Tana ganin ta zo kan layin gidan kuma ta tabbatar ba kowa a kusa da gun saboda layi ne mara hayaniya ko da ba dare ba ruwan sama sai ta zuba da gudu ta shige gidan. Ba ta yi birki a ko’ina ba sai a ɗakin Innare jiki na rawa ta sauya kayan jikinta zuwa zani da zumbuleliyar rigar kakar tata ta rufa a kan gadon.
Da dare wuraren ƙarfe sha ɗaya na dare bayan malam Shu’aibu ya dawo gida matarsa Hadiza ta zaunar da shi tana labarta masa magana a kan batun Ahmad da Surayyah, da saƙon shi da ta riska.
Shi ma ya ji ba daɗi a ransa domin tun bayan samuwar Ahmad a cikin rayuwar ‘yarsa ya lura da ƙaruwar walwalarta ya kuma saka fata a kan cewa wannan shi ne mijinta da suka jima suna jiran bayyanar shi.
A nan dai take yi masa bayani game da kuɗirinta ta ce “Da ma Malam wata ‘yar shawara nake tafe da ita game da lamarin nan.”
Da ido ya kafe ta yana furta “To ina jin ki.”
Kanta na ƙasa ta fara magana “Malam na ce me zai hana ka kira Ahmad ka yi magana da shi baka da baka a kan al’amarin ko za mu san dalilinsa na janyewar?”
“A’a Dije ba za a fara wannan karen aikin da ni ba, kin ga fa ko baikonsu ba a yi ba ballantana a ce manya sun shiga cikin lamarin yayin ƙullawa yanzu ma gun kwancewa a saka su. Ba mamaki ya sauya ra’ayi ne a kanta kawai ko ya samo wacce ya ga ta fiye masa ita.”
Girgiza kai ta yi alamun bai fahimce ta ba sai ta sake cewa “Ya kamata ka fahimce ni malam yana da kyau mu san me ke faruwa, idan kai ba za ka iya ba zan saka Mustapha ya yi masa magana amma fa sai idan ka amince.”
“Yanzu ki ga dawo kan layi, maganarsu ce ta ‘yan bana-bakwai zai iya, amma ni idan na yi abin zai yi wani irin bambarakwai wai mace da suna Ummaru.” Ya ɗan yi shiru yana gyara kishingiɗarsa a kan gadon kafin ya sake cewa.
“Ke ma dai kin so saka damuwa a ranki ne.
Haba sai ka ce yarinyar da muka gaji da ita muke neman mararraba da ita?”
Daga haka suka ajiye wannan caftar suka zaro wata suna hirarrakinsu irin na mata da miji har bacci ya yi gaba da su.
Kashegari tun sassafe wuraren 7:30
mama ta kira Mustapha ta saka shi wannan aikin da ta kuɗurta a ranta kuma ya yi na’am ya yi biyayya ga zancensa. Da kansa ya kira Ahmad wuraren sha ɗayan rana ya faɗa masa yana so su haɗu akwai ɗan abin da yake so su tattauna a kai.
Duk da Ahmad ya san cewa tatsuniyar gizo ba ta wuce ta ƙoƙi amma sai ya karrama Mustaphan ya ba shi dama da adireshin inda za su haɗu.
Da misalin ƙarfe 2:30 na rana suka haɗu a inda suka tsara suka gaisa a mutunce cikin girmama juna a nan Mustapha ya tuntuɓe Ahmad game da batun Surayyah da abin da ya faru tsakaninsu ya janye maganar auren su kamar yadda suka ji labari a bakinta.
Busasshen murmushi ya yi kafin ya kalli Mustapha da yake hasashen ba za su wuce sa’anni ba ya ce “Ka da ku zargi Surayyah ba ta yi mini komai ba.
Kawai dai na yanke hukuncin ne bayan yin dogon nazari game da makomar rayuwata. Ina ƙaunar Surayyah har gobe sai dai aurenmu zai iya zuwa da damuwa a gaba. Kamar yadda na faɗa mata ne ina da ƙwaƙƙwaran dalili da na bar wa kaina sani, kuma ko da mutane dubu ne za su zo da wannan tambaya amsata ba za ta sauya ba.”
Tun lokacin da ya fara zancen Mustapha ya ƙure shi da ido yana so ya karanto gaskiya a cikin idon nasa, amma ga dukkan alamu shi ƙwararren pretender ne don har ya kammala Mustapha bai iya tantance gaskiyar tasa ba.
Yana gama jawabansa kuwa ya miƙe yana shirin barin gun, Mustapha bai yi yunƙurin dakatar da shi ba sai gyara zamansa da ya yi kan kujerar robar da ke ajiye a cikin ɗakin cin abincin yake zaune a kanta ya zuba tagumi yana bin Ahmad da ido har ya fice daga ɗakin cin abincin.
Sai da ya ƙara tsotse smoothie ɗin hannunsa sa’annan nan ya miƙe ya shi ma ya bar restaurant ɗin gabaɗaya.
Daga can bai zame ko’ina ba sai gidansu ya yi wa mamansu bayanin komai ya ƙara da faɗar “Na fuskanci akwai abin da yake ɓoyewa a ransa, amma ban iya gano ko miye ba. Idan ba damuwa mama ina so a yi jana’izar rayuwar Ahmad a gidan nan, ko labarinsa kada a ƙara tadawa.”
Ba haka mama Hadizan ta so ba, to amma ya za ta yi da abin da ya fi ƙarfin wuta? Sai dai fa har a lokacin ba ta yarda cewa Surayyan ba ta da laifi ba ko da kuwa a ce duk jikinta kunne ne, za dai ta ji dole yarda babu.
A daidai wannan lokacin ne kuma Surayyar ta shigo gidan ta samu maman tsaye a ƙofar ɗakinta “Ke da ga ina kike ne?”
Da fara’a kaɗan a fuskarta ta ce “Daga gidansu Zainab nake na je aro wannan littafin?” Ta ɗaga novel ɗin da ke hannunta tana nunawa Mama.
Maman ta bi ta da kallon nakasa irin wanda ba ta so ta ga maman ta yi mata shi, amma ta lura ita ƙoƙari take ta mayar da kallon ta zama ɗaya daga cikin ɗabi’unta.
“Haka kika iya dama, wato ke ko a jikinki? Jiya-jiyan nan kika gama koke-koken rabuwa da wanda zai aure ki amma har kin manta za ki fara sharholiya? Tsaya ma tukunna ko dai a cikin ire-iren waɗannan littattafan kike koyo hanyoyin kore manema aure cikin sauƙi?”
Sororo kawai Surayyan ta yi tana ta kallon maman. Iya zahirinta kawai mutane suke iya gani da a ce za su iya tona zuciyarta su ga tarin damuwar da take ciki da za su fahimci cewa duka ta fi su buƙatar ta yi auren a daidai wannan gaɓar.
Yanzu ma ta je ta aro wannan littafin ne domin ya rage mata kewa da damuwar da take ciki. Tana so ta koyawa kanta rayuwa babu Ahmad tare da mantawa da wanzuwar sa a doron duniya shi ya sa ta yanke hukuncin ƙirƙirar sabbin abubuwa irin su kallo, karatu da wasanni a waya domin su ɗauke hankalinta a kan tunaninsa.
Murmushin kan fuskarta ma da ta shigo da shi gidan na bogi ne don kawar da hankalin masu kallonta.
Ba ta tamka ba ta wuce ɗaki ta yasu a ƙasan kujera ta ɗaga kanta ta baya ta ɗora a kan seat ɗin kujerar.
Daga can waje ta jiyo maman na faɗar “Wato ga mahaukaciya na magana ko? Ah lallai dole kya wuce. Bar jin Ahmad ya ɗaurewa karyarki ƙugu yana cewa iska ne da ke, ni sam ban yarda da wannan tatsuniyar ba, ko da ma akwai ciwon to ya tarar da hali.”
“Ba wani iska sai iskanci a kanta.” Ta tsinto muryar Aysher daga waje tana faɗawa mama.
Zancen ya matuƙar ƙona mata rai kamar ta fito ta dad-dallawa Ayshern mari sai dai tun kafin ta yanke hukuncin abin yi ta tsinto muryar mama da ke tunkaro ɗakin tana faɗar “Ki bar ta kawai, auren ne ba ta son yi ta fi son mu zauna muna gwada kafaɗa da ita. Allah ya bada sa’a Surayyah ki ƙara shekara goma ma a gidan in kin so ga fili nan ga mai doki…”
Ba ta san ya aka fara ba zuciyarta ta kasa yin juriya a wannan karon sai tsintar kanta ta yi da ɗaga murya tana faɗar “Ba na fata mama, in Sha Allahu wannan fatan ba a kaina ba sai dai a kan ‘yar so, Autarki.”
Mama ta zo daidai ƙofa kenan da niyyar shiga ciki zafafan kalaman Surayyar da suke baƙi a kunnenta suka yi zuf suka shige kunnuwanta. Ta ƙame a gurin tamkar matacciya da tufafi tana ƙarewa fuskar Surayyan kallo, sai cika take tana batsewa wanda sam wannan ba halinta ba ne.
Ummu Intisar ce
