Meke kawo rikice rikicen zaman aure a wannan zamanin?
Kashi na farko!
Akwai abubuwa da dama da suke kawo rikice-rikicen zaman aure a wannan zamani da muke ciki. Galibi matsalar ba wai rashin soyayya kaɗai ba ce, har da rashin fahimtar juna da hakkokin juna, rashin haƙuri da sauran abubuwa.
Rashin fahimtar juna;
Wasu ma’aurata ba sa iya fahimtar ra’ayin juna. ba’a girmama ra’ayin juna sam!Ƙaramin abu kan zama babban rikici saboda rashin tattaunawa cikin natsuwa, ko kuma rashin tattaunawa nan take a kan lokaci.
Da ace duk yadda ƴar matsala ƙarama ta kunno za’a zauna a tattauna a samu sulhu da tabbas za’a ji sauƙi a wannan ɓangaren.
Sulhu cikin natsuwa, girmama ra’ayin juna tare saurin ɗaukar laifin da yake naka kan gyara kaso goma daga cikin rikice rikicen zaman aure a wannan zamanin!
Managarciya!
