Jam’iyyar adawa ta PDP ta tsayar da Alhaji Abubakar Abdullahi matsayin ɗan takarar gwamnan Sakkwato, a wata matsaya da aka cimma ta sulhu a hidikwatar jam’iyyar a birnin jihar.Alhaji Isah Tudun Falala ne jami’in gudanar da zaɓen ya ce a sulhun da aka cimma an yarda da ɗan takara guda ta hanyar sasanci ba wani mai ƙorafi a kai.
Bayan kaddamarwar ɗan takarar gwamnan ya ce zai yi ƙoƙarinsa in ya samu nasara ya fitar da jihar daga cikin ƙangin talauci da take fama da shi, “ka duba a ƙididdiga fa an fito da bayanin a duk Nijeriya Sakkwato ce jiha mafi talauci bayan kuma muna da albarkatun ƙasa da duk in da akwai su wurin zai zama mai arziki, muna da sinadarai da ke mayarda hamada dausayi, Tafarnuwa Sakkwato a duk Duniya tana ta farko, muna da arzikin man fetur, duk da waɗan nan arzikin amma mun koma baya har muna riƙe da kambin Talauci,” a cewarsa.
Ya ce “ƙoƙarin da muke da shi abi hanyar da za a fitar da mutane a cikin talauci, shi ne manufarmu a tafiyar mu.”
Shugaban jam’iyyar a jiha Hayatu Tafida ya ce ɗan takarar PDP sananne ne a Sakkwato wanda yake da ƙwarewa a fannoni da dama, kana ganin yanda yake faɗar kididdigar talauci a Sakkwato.
“Ɗan takara shi ke sayar da kansa, yana da ƙwarewa, da ganin dacewar a riƙa koyar da yara a makaranta da harshen mahaifiya, hakan ya kawo taɓarɓarewa karatun yara sun koma barace barace kan hanyoyi, in ba a ɗauki mataki ba nan da shekara 15 Allah ne ya san halin da jihar za ta shiga,” kalaman shugaban jam’iyya.






