Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci INEC da hukumomin tsaro su tabbatar da cewa zaɓen gwamnan jihar Osun da za a gudanar a gobe Asabar, 15 ga watan Agusta, 2026, ya kasance cikin lumana, gaskiya da adalci.
A cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Juma’a, Tinubu ya ce INEC na da alhakin tabbatar da sahihancin tsarin zaɓen da kuma kare amincin sakamakonsa.
Shugaban ya kuma buƙaci INEC ta yi amfani da zaɓen Osun a matsayin gwaji na nuna shirinta na gudanar da babban zaɓen 2027 cikin inganci.
Haka kuma, ya umarci Rundunar ’Yansandan Najeriya da sauran hukumomin tsaro da aka tura jihar Osun da su tabbatar da tsaron masu kaɗa ƙuri’a da jami’an zaɓe, tare da hana duk wani mai tayar da hankali kawo cikas ga gudanar da zaɓen.
Tinubu ya ƙarfafa wa al’ummar Osun gwiwa da su fito su kaɗa ƙuri’unsu cikin ’yanci, ba tare da tsoro ko barazana ba.
Ya jaddada cewa sakamakon zaɓen dole ne ya kasance abin da ya dace da zaɓin al’ummar jihar Osun, yana mai cewa sahihancin zaɓen zai dogara ne kan yadda sakamakonsa zai nuna muradin masu kaɗa ƙuri’a.





