Kodinetan Remi Tinubu a Sokoto ya shirya gasar ƙwallon ƙafa saboda takarar Sanata ta Ajiyan Isa
Matashin ɗan siyasa a Sokoto kuma Kodinetan Remi Tinubu Alhaji Abdul Tamaje ya shirya gasar ƙwallon ƙafa ga matasan jiha domin nuna gamsuwa da amincewar sa ga takarar Sanata a yankin Sokoto ta Gabas da Alhaji Umaru Ajiyan Isa yake yi a zaɓen 2027.
Gasar da aka kammala a ranar Lahadi an baiwa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Basu da ta zo ta ɗaya Rago babba na kimani dubu 350, sai ta biyu ta samu buhun shinkafa mai KG50 da kuɗi dubu 100, an baiwa sauran ƙungiyoyi da suka fafata a gasar ƙwallon ƙafa mai tsada.
Alhaji Abdul ya ce “mun shirya wannan gasar da kuma nuna ƙauna da soyayya ga mai gidanmu Alhaji Umaru Ajiya kan takararsa ta Sanata, bayan wannan mun shirya abubuwan taiamakon matasa sosai da za mu gabatar, ba za mu bari ba har sai burinmu na ganin matasa sun zama masu dogaro da kansu ya cika,” kalaman Abdul Tamaje.
Ɗan takarar ɗan majalisar dokokin jiha da zai waƙilci ƙaramar hukumar Isa cikin jam’iyyar APC Honarabul Auwal Umar Walin Isa ne ya bayar da kyaututtukan ya ce kamar yadda kowa ya sani harkar wasanni na cikin abin da ke haɗa kan matasa, “Abdul Tamaje ya ga yakamata ya ba da tasa gudunmuwa domin cigaban tafiyar Ajiyan Isa ɗan takarar Sanatan Sokoto ta Gabas wannan abin yabawa ne, an kammala wasa lafiya.
“Wanda aka shirya wasan saboda shi, yana baiwa harkokin matasa muhimmanci sosai hakan ya sanya yake tura yara ƙasashen waje domin wasanni, ba ƙaramin cigaba ba ne matasanmu su riƙa samun dama suna buga wasa a wajen Nijeriya, saman wannan lamari yake kuma zai ci gaba da yin haka.” Auwal Walin Isa




