Home Labarai Mutanen da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su Masallacin Juma’a a...

Mutanen da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su Masallacin Juma’a a Neja suna cikin matsala

31
0

Yan ta’adda sun yi garkuwa da mutane da dama a masallatai hudu yayin gudanar da sallar Juma’a a wasu al’ummomi na ƙaramar hukumar Borgu da ke Jihar Neja.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a a garuruwan Dekara, Kpenya, Sabon-Gida da Gidan-Zana, inda ’yan ta’addan suka mamaye masallatan a lokaci guda tare da kwashe masu ibadar zuwa daji.

Wani mazaunin yankin ya ce a Dekara kaɗai, an yi garkuwa da fiye da mutum 60 a babban masallacin garin, yayin da wasu rahotanni suka ce sama da mutum 100 daga Gbezhin ba a san inda suke ba.

A wani faifan bidiyo da ’yan ta’addan suka fitar, sun yi iƙirarin cewa sun yi garkuwa da kusan mutum 500, ciki har da mata da yara. Sai dai har yanzu ba a tabbatar da wannan adadi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here