Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar, ya shaida wa hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka (FBI) cewa ’yan Nijeriya ba za su amince da amfani da kalmar “barazana ga rayuka” a matsayin hujjar ɓoye bayanan da ka iya kasancewa na bayyanawa ga jama’a, musamman wadanda suka shafi shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Cikin wata sanarwa da hadiminsa na musamman Phrank Shaibu ya fitar, Atiku ya jaddada cewa ya kamata batutuwan da suka shafi shugaban ƙasa da bayanan jama’a su kasance cikin sahihanci da gaskiya.






