An kammala sukuwar Dawaki ta Nijeiya karo na 12 wadda kungiyoyin gasar tsren Dawaki ta Afirika ke shirya lokaci bayan lokaci wadda a wannan karon aka yi a jihar Sakkwato.
Wasar sukukuwar da aka gudanar an yi nasarar cin kofin Sarkin Musulmi da Sanata Wamakko da Gwamnan Sakkwato da shugaban ƙasar Najeriya in da aka yi nasara samu kyauta sama da miliyan 30 da kofuna da motoci shidda a tsakanin manyan matakan da jamhuriyar Nijar da jihohin Sakkwato da Kano da Kaduna da Kebbi suka fafata.
Kofin Sanata Wamakko Dawaki Takwas suka shiga tseren waton, Ƙara da kiyashi da fast and fast da Sa-gari kuka da Ɓagone daga Nijar da Ja’inja daga Sakkwato da Dan Ashana, Kano, da sauransu.
A ɓangaren na ɗaya: Ɗan Ashana ne na Salim Sani Buhari, na biyu Ɓagone na Abubakar Mai duka, na uku Kara da kiyashi na Badamasi. Gudun an yi shi ƙasa da minti uku, mita dubu biyu.
Sai kofin Gwamna na daya, Doki mai suna Messi na Faruku Burona, na biyu etiwal na Hussaini daga Yamai na uku ba’a bayyana ba domin an kasa fitar da wanda ya yi nasara kan yadda dawaki uku suka zo kunnen doki.
Kofin shugaban ƙasa wanda shi ne matakin karshe na ɗaya doki Leader na Suleimma Faruku Mayana daga Sakkwato, sai na biyu Faris na Salim Sani Buhari, Kano, 3 Old Star boys shima Kano. Sanata Aliyu Wamakko ya yi jawabin godiya ya ce wannan ba sabon abu ba ne tseren dawaki tarihi ya san da shi a Sakkwato, al’adar mutanen jihar ne.
Ya ce Gwamna ya ce za a inganta filin da za a riƙa gudanar da kowace sukuwa ake buƙata ta ƙasa da ƙasa.
Sanata Wamakko ya baiwa duk Dokin da ya yi nasara miliyan biyu in da ya baiwa wanda ya zo na ɗaya a matakin na shugaban ƙasa miliyan biyar.Sukuwar dawaki na cikin wasannin da matasa a jihar ke shauƙin kallo da ba ta muhimmanci.





