Home Rahoto Gwamnatin Tinubu ta faɗi hasarar da za ta yi in aka mayar...

Gwamnatin Tinubu ta faɗi hasarar da za ta yi in aka mayar da litar Mai 500

28
0

Gwamnatin Tinubu Tace Idan Aka rage farashin litar man zuwa naira ₦500 kan lita zai Ayi Asarar sama da tiriliyan ₦16trn a shekara –Gwamnatin Tinubu

Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta bakin ministan Kuɗi Oyedele ya bayyana cewa dawo da tallafin man fetur domin sayar da shi kan ₦500 a kowace lita zai jawo wa Gwamnatin Tarayya asarar kuɗaɗen shiga da suka haura naira tiriliyan 16 a duk shekara.

Oyedele ya bayyana cewa irin wannan mataki zai haifar da babban nauyi ga kuɗaɗen gwamnati, wanda zai iya shafar yadda ake samun kuɗaɗen gudanar da sauran muhimman ayyuka.

Wannan bayani na zuwa ne yayin da ake ci gaba da muhawara kan farashin man fetur da kuma hanyoyin da za a bi domin rage wa ’yan Najeriya nauyin tsadar rayuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here