Gwamnatin Shugaba Tinubu Tace dole a tausawa ‘yan Najeriya daga yanzu za ta rinka sayar da litar man fetur mai ruhusa ga ‘yan Najeriya don rage tsadar rayuwa kan Naira 1,350 na tsawon kwanaki 30
Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin rage farashin man fetur da ake sayarwa a gidajen mai na kamfanin NNPC, inda za a yi wannan rangwame na tsawon kwanaki 30, tare da ba masu safarar fasinjoji fifiko.
Ministan Kuɗi kuma mai kula da tattalin arzikin ƙasa, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan a Abuja, inda ya ce gwamnati na shirin sanya iyakar kuɗin da za a sayar da man fetur ga masu tacewa ko shigo da shi zuwa Naira 1,350 kan kowace lita.
Ya bayyana cewa wannan mataki ba yana nufin dawo da tallafin man fetur ba ne, sai dai wani tsari ne da zai ba kamfanin NNPC damar sayar da man a kan kuɗin da ya kashe wajen samunsa, ba tare da ƙara ribar sayarwa ba a lokacin rangwamen.
Gwamnatin ta kuma bayyana cewa za a riƙa duba farashin a kowane wata domin daidaita shi da yanayin kasuwa.
Baya ga haka, gwamnati na shirin samar da ƙarin ɗanyen mai ga matatun man fetur na cikin gida domin rage tasirin sauye-sauyen farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya.
Sai dai tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki matakin, yana mai tambayar abin da zai faru bayan kwanaki 30 ɗin sun ƙare, tare da cewa rangwamen na ɗan lokaci ba zai magance matsalolin tsadar sufuri da kayan abinci da al’umma ke fuskanta ba.
Haka kuma, jam’iyyar NDC da ƙungiyar yaƙin neman zaɓen ADC sun soki matakin, inda suka bayyana shi a matsayin wani mataki da bai wadatar wajen magance matsin tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke ciki ba.
Rahoton Vanguard ya bayyana cewa rangwamen zai shafi gidajen mai na NNPC, yayin da gwamnati ke fatan sauran ‘yan kasuwar man fetur za su yi koyi da wannan mataki domin rage wa al’umma nauyin tsadar rayuwa.






