Home Labarai Rage farashin fetur da NNPC ta yi ba dawo da tallafin mai...

Rage farashin fetur da NNPC ta yi ba dawo da tallafin mai ba ne – Gwamnatin Tinubu

120
0

Rage farashin fetur da NNPC ta yi ba dawo da tallafin mai ba ne – Gwamnatin Tinubu

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa rangwamen farashin man fetur da kamfanin NNPC ya fara yi tun ranar 1 ga Oktoban 2026 ba yana nufin dawo da tallafin man fetur ba ne, domin babu kudin gwamnati da ake kashewa wajen aiwatar da rangwamen. A wata sanarwa da Ministan Kudi, Taiwo Oyedele, ya fitar ranar Juma’a, ya bayyana cewa kamfanin ya rage ribar da yake samu daga sayar da kowace litar fetur ne domin saukaka wa masu amfani da man, ba tare da gwamnati ta biya wani bangare na kudin ba.

Ministan ya kara da cewa matakin na iya taimaka wa NNPC wajen kara yawan kwastomomi da tallace-tallace, wanda hakan zai iya bunkasa ribar kamfanin a nan gaba. Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba ta da shirin dawo da tsarin tallafin man fetur da ta soke a shekarar 2023. A cewarsa, gwamnati na ci gaba da daukar wasu matakai domin rage radadin tsadar sufuri da makamashi, ciki har da fadada amfani da motocin gas na CNG da kuma cire wasu haraji da kudaden da ke kara tsadar man fetur.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here