Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Rotimi Amaechi, ya kalubalanci gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan yadda tsadar rayuwa ke kara ta’azzara, yana mai cewa cire tallafin man fetur ba tare da samar da isassun matakan rage radadin hakan ba ya kara jefa ‘yan Nijeriya cikin mawuyacin hali.
Amaechi, tsohon gwamnan jihar Rivers kuma Dan Amanar Masarautar Daura a jihar Katsina, ya bayyana hakan ne yayin wata hira a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels TV.
Ya ce a shirye yake ya janye daga matsayin abokin takarar Atiku Abubakar, ya koma yakin neman zaben Tinubu, muddin farashin litar fetur ya sauka zuwa Naira 600 kafin ranar Asabar.





